Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 22:16:53    
Wasannin Olympic na nakasassu kasaitaccen biki ne da ke kawo wa 'yan Adam zaman lafiya da zumunci

cri

A cewar Mr.Sidialo, a gun wasannin Olympic na Beijing da aka rufe kwanan baya ba da jimawa ba, tawagar 'yan wasan Kenya ta sami lambobin zinariya 5 da na azurfa 4 tare kuma da na tagulla 4, har ma ta zo na 15 a tsakanin kasashen duniya a wajen yawan lambobi, kuma tana matsayi na farko a tsakanin kasashen Afirka. Wannan kuma ya karfafa gwiwar 'yan wasa nakasassu na kasar. Ya ce, " 'yan wasa nakasassu na Kenya sun nuna gwanintarsu a gun dimbin manyan gasannin duniya, kuma za su yi iyakacin kokarinsu wajen shaida wa duniya cewa, ba ma kawai tawagar 'yan wasan Kenya za ta iya samun nasarori a Beijing ba, haka kuma 'yan wasa nakasassu na Kenya ma za su sami sakamako mai kyau, ba za su ja da baya ba."

Samun lambobin yabo da jawo wa kasarsa alfarma buri daya ne na 'yan wasa baki daya, amma a ganin Mr.Sidialo, ban da lambobin yabo, wasannin Olympic na nakasassu na da karin muhimmanci ga 'yan wasa nakasassu. Ya ce, a yayin da 'yan wasa nakasassu ke dinga kalubalantar kansu da kuma samun nasara, sun maido da imaninsu ga zaman rayuwa. Sa'an nan, wasannin Olympic na nakasassu ya kafa wani dandali ga nakasassu na duk duniya a wajen fahimtar juna da karfafa dankon zumunci. Mr.Sidialo ya ce, " 'yan wasan da suka zo daga kasashe da shiyyoyi daban daban na duniya sun karfafa dankon zumunci a tsakaninsu a gun wasannin Olympic na nakasassu, kuma ba shakka, irin zumunci ya fi dadewa. A ganina, wasannin Olympic na nakasassu kasaitaccen biki ne da ke kawo wa 'yan Adam baki daya zaman lafiya da fatan alheri da kuma zumunci."(Lubabatu)


1 2