Saboda rauni mai tsanani da ya samu a sakamakon motsa jiki, Hu Jia, 'dan wasa na kasar Sin, wanda ya taba samun lambar zinariya a wasan tsalle cikin ruwa na mita goma na wasannin Olympics na Athens, ya rasa damar shiga wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008. Amma duk da haka, a cikin mutane masu yawo da fitilar wasannin Olympics dake zangon Wuhan, wato hedkwatar lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin, har ila yau dai, mutane sun yi farin ciki matuka da ganin wancan saurayi wato Hu Jia, wanda cike yake da imani yayin da yake rike da fitilar wasannin a cikin hannunsa.
Hu Jia wani jarumi ne a zuciyoyin masu sha'awar motsa jiki. A gun wasannin Olympics na Sydney da aka shirya shekaru 8 da suka wuce, Hu Jia, wanda a karo na farko ne ya shiga irin gasar ya samu lambobin azurfa, tun daga lokacin kuma, Hu Jia ya yi ta samun nasarori a fannin daka tsalle cikin ruwa. A gun wasannin Olympics na Athens da aka shirya a shekarar 2004, Hu Jia ya yi fice wajen gasar karshe ta tsalle cikin ruwa na mita goma, haka kuma ya samu lambar zinariya mai daraja ga kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin. Saboda sakamako mai kyau da Hu Jia ya samu wajen motsa jiki, don haka, aka zabe shi ya zama mai yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing, kuma ya koma garinsa, birnin Wuhan, don halartar bikin yawo da fitilar a wurin. Kwanan baya, an samu babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, wannan ya sa Hu Jia ya kara yin tunani kan ma'anar yawo da fitilar wasannin Olympics. Ya ce,
"Hasashen yawo da fitilar wasannin Olympics shi ne, karfafa zafin nama, da more buri, a ganina yanzu yana da ma'ana daban, wato nuna kauna da fatan alheri ga jama'ar yankuna masu fama da bala'in. Muna fatan gaya musu cewa, wajibi ne su sa kaimi har zuwa karshe a cikin hali mai tsanani, kuma su yi yaki da bala'in har zuwa karshe."
A idon kwararru a sana'ar musamman, fasahar da Hu Jia ya nuna a fannin wasan tsalle cikin ruwa ta more mutane kwarai da gaske, saboda haka, ya taba zaman shugaban 'yan wasan tsalle cikin ruwa na mita goma a nan kasar Sin. Hu Jia ya fahimta sosai wajen samun daidaito tsakanin wahalar fasaha da zama mai karko a fannin nuna wasan tsunduma. Ya ce,
"A ganina, samun daidaito tsakanin wahalar fasaha da zama mai karko, wannan na dogara ne da fahimtar da muka samu wajen tsalle cikin ruwa. Ya kamata ka yi tsunduma bisa karfinka. Idan kana son neman wahalar fasaha kawai, amma ba bisa karfinka ba, to ko shakka babu za ka ci tura a gasa."
Hu Jia ya zama jarumi a fannin tsalle cikin ruwa bayan da ya shiga gagaruman wasanni na duniya fiye da goma, lallai ya samu wadannan nasarori ne saboda ya yi ta yin kokari a rayuwarsa ta harkar yin tsalle cikin ruwa har cikin shekaru 20. Saboda yana ayyukan tsalle cikin ruwa cikin dogon lokaci, don haka, ya taba samun wani irin ciwon ido, bayan da aka yi masa tiyata, sai ya janye jikinsa daga gasa har kusan shekaru biyu. Amma, domin shiga wasannin Olympics na Beijing, ya farfado da aikinsa na tsalle cikin ruwa na mita goma. Hu Jia, wanda ke mayar da aikin tsalle cikin ruwa irin wasa a matsayin raywarsa ya ce,
"Ina kaunar tsalle cikin ruwa sosai, ina daukar da shi a matsayi na sha'anin da nake so. Saboda haka, duk ko wane irin rauni da nake ji, duk ko wane irin ciwon da na samu, zan yi iyakacin kokarina, don kawar da wahaloli, ta yadda zan iya sake halartar gasar tsalle cikin ruwa ta mita goma."
Amma, abin bakin ciki shi ne, raunin gwiwa mai tsanani da yake ji ya kawo tasiri sosai ga sakamakon da ya samu a gasar zaben zakaran wasannin Olympics da aka shirya a shekarar da muke ciki. Kan halin da yake ciki a yanzu, Hu Jia ya kusan rasa damar shiga wasannin Olympics na Beijing, amma ya gaya wa wakilinmu cewa, da kyar ya bar aikin tsalle cikin ruwa. Ko da ya ke ba zai iya halartar wasannin Olympics na wannan karo ba, amma yana son tsayawa kan aikin tsalle cikin ruwa ta mita goma har shekaru hudu, don neman damar shiga wasannin Olympics na London da za a shirya a shekarar 2012.
"Ina da zafin nama sosai kan wannan, amma zan tabbatar da shi ne bisa halin lafiya da jikina ke ciki. Yanzu na samu sauki kan raunina, amma ban iya tabbatar da halin da nake ciki a shekaru hudu masu zuwa ba. Saboda haka sai dai na iya cewa, ina fatan shiga wasannin Olympics na London, zan yi kokari kan wannan."
|