Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 20:27:14    
Beijing ta sa kaimi kan bunkasuwar sha'anin nakasassu ba tare da tangarda ba

cri

Yanzu a nan Beijing, akwai cibiyoyin musamman 150 da ke biyan bukatun nakasassu a fannonin warkar da jikinsu da samun aikin horo domin samun aikin yi da kuma harkokin nishadi da kuma kiyaye iko da moriyarsu. Madam Zhao ta ba da misali cewa,'Makaho sun iya koyon fasaha a wadannan cibiyoyi. Wasu daga cikinsu sun bude shaguna a kan Internet. Sa'an nan kuma, nakasassu sun iya wasan kwallon tebur a cibiyoyin. Sun iya samun jiyya ta fuskar tunani daga lokitoci masu ilmin warkar da tunani a cibiyoyin, ta haka, sun iya daidaita matsaloli da wahalhalun da suke fuskanta yadda ya kamata.'

Chen Xiaojing ita ce uwar wani yaro da ya nakasa a kwakwalwa. Ta gaya mana cewa, yaronta ya kan je irin wannan cibiya a unguwar da suke zama domin samun aikin horo, ya riga ya sami ci gaba sosai. Madam Chen ta ce,'Malamai sun koya musu kidaya da wanke tufafi da dafa abinci, sun koya musu yin abubuwan da suke iyawa. Musamman ma sun koya musu wasu ayyuka masu sauki. Ban da wannan kuma, an biya su kudade bayan ayyuka a ko wane wata, ban taba tsammani haka a da ba.'

Madam Zhao ta ci gaba da cewa, wadannan cibiyoyin musamman 150 a nan Beijing su ne abubuwan koyi kawai, ana ci gaba da neman raya su. Nan gaba yawan irin wadannan cibiyoyin musamman zai yi ta karuwa, kuma matsayinsu na ba da hidima zai samu kyautatuwa ba tare da kasala ba.(Tasallah)


1 2