Kasar Korea ta Kudu wata kasa ce da ta taba zama cikin mulkin mallaka, inda aka taba tayar da yakin basasa domin neman kawo wa kasar baraka, haka kuma ita wata kasa ce da ta ki bude kofa ga waje a gwargwado. Ko da yake ta samu babban ci gaba wajen tattalin arziki, amma kafin wasannin Olympics, duniya ba ta san kasar sosai ba balle ma dogon tarihi da kyawawan al'adunta. Park She Jik, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Seoul ya bayyana cewa, sabo da haka, kasar Korea ta Kudu ta mayar da aikin shirya wasannin Olympics a matsayin wata kyakkyawar damar kyautata fuskarta. Kuma ya kara da cewa, "A gun gasar wasannin Olympics ta Seoul, an gabatar da kirari na 'duniya ta shiga birnin Seoul, kuma birnin ya fita zuwa duniya'. Kuma gasar ta zama wata kyakkyawar dama gare mu wajen koyon sakamako mai kyau na duniya da kuma gabatar da kasar Korea ta Kudu ga duk duniya."
Ban da wannan kuma Mr. Park She Jik ya bayyana cewa, domin daga kwarjinin kasar Korea ta Kudu, kasar ta tsara wata ka'ida, wato karbar sakamako mai kyau da sauran kasashe suka samu bisa tushen mayar da al'adun kasar Korea ta Kudu a matsayin cibiya domin nuna al'adun kasar ga jama'ar duk duniya. Kuma wanda ya fi shaida ka'idar sosai shi ne yunkurin wallafa waka ta babban take ta gasar wasannin Olympics ta Seoul mai taken "hannu da hannu", wadda har yanzu take samun karbuwa sosai daga duk duniya. To yanzu bari mu saurari wani karamin kashi na wannan waka tare.
Ban da wannan kuma, Mr. Park She Jik yana ganin cewa, gasar wasannin Olympics ta Seoul wata gasar wasannin Olympics ce da ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa, da kuma sanya kasar Korea ta Kudu cikin kasashe masu matsakacin matsayi na ci gaba. Kuma ya ce, "gasar wasannin Olympics ta Seoul ta samar da wata kyakkyawar dama wajen yada labarun kasarmu ga duk duniya. Kuma ta shirya gasar, kasar Korea ta Kudu ta bayyana saurin bunkasuwarta a cikin shekaru 30 bayan yakin basasa na zirin Korea, ta haka an canja ra'ayin mutane kan Korea ta Kudu, da kuma karfafa kwarjinin kasar a duniya. Bugu da kari kuma shirya gasar cikin nasara ta kara kwarin gwiwar 'yan kasar, kuma sun fahimci cewa, muddin an hada gwiwa tare, to tabbas ne zai samu nasara, Wanda ya zama daya daga cikin sakamako mafi kyau da gasar wasannin Olympics ta Seoul ta kawo mana."
|