Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 19:42:32    
Beijing ta sa kaimi kan bunkasuwar sha'anin nakasassu ba tare da tangarda ba

cri

Ran 3 ga wata, a nan Beijing, Zhao Chunluan, jami'ar hadaddiyar kungiyar nakasassu ta birnin Beijing ta bayyana cewa, a shekarun baya, Beijing ta sami babban ci gaba wajen raya sha'anin nakasassu, za ta kuma yi ta kyautata shi a nan gaba.

Yanzu nakasassu kusan miliyan 1 suna zama a nan Beijing, yawansu ya wuce kashi 6 cikin dari bisa jimlar mazauna Beijing, mutane kimanin miliyan 2 da dubu 600 suna zama tare da su a cikin iyalai. Wadannan nakasassu suna kasancewa rukunin musamman mai yawan mutane, suna matukar bukatar taimako daga saura.

Madam Zhao ta yi karin bayani da cewa, a shekaru da dama da suka wuce, hukumomin kasar Sin a matakai daban daban sun zuba kudade da yawa, sun kuma fito da jerin manufofi domin kyautata zaman rayuwar nakasassu da kiyaye iko da moriyarsu. Kasar Sin ta sami babban ci gaba wajen raya sha'anin nakasassu. Birnin Beijing shi ma ya sami irin wannan babban ci gaba. Madam Zhao ta ce,'Wadannan manufofi sun shafi ba da tabbaci ta fuskar zaman al'ummar kasa, da sa kaimi kan samar wa nakasassu guraban aikin yi, da kuma tabbatar da ganin nakasassu sun iya shiga harkokin zaman al'ummar kasa cikin adalci da dai sauransu.'

Kamar yadda madam Zhao ta fada, wadannan manufofi suna taimakawa nakasassu a zaman rayuwarsu daga fannoni daban daban. Ga misalin zirga-zirga, domin bai wa nakasassu saukin tafiye-tafiye, Beijing ya tsara ka'idojin raya da kula da na'urori marasa shinge, yana kiyaye ikon nakasassu ta fuskar tafiye-tafiye bisa dokoki. Sa'an nan kuma, ya shimfida sabbin hanyoyi da kuma gina sabbin na'urorin al'umma tare da na'urori marasa shinge. Madam Zhao ta ce, saboda kusantowar gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, an gaggauta gudanar da wadannan ayyuka. Ta ce,'A fannin zirga-zirga ba tare da shinge ba, Beijing ya yi amfani da bus-bus marasa shinge 2835 da kofofinsu suka yi kasa sosai domin yin jigilar fasinjoji. Haka kuma, zai yi amfani da bus-bus din musamman guda dari 6 da suka iya daukar kekunan hannu 6 a lokaci guda a lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Ban da wannan kuma, an tabbatar da kawar da shinge a cikin dukkan bus-bus da ke tafiya a hanyoyi 2 masu saurin tafiya.'

1 2