Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 19:41:33    
Wani bikin da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin "Mangzhong" cikin Sinanci

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samuwa da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci, ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.

Bikin "Mangzhong" cikin harshen Sinanci shi ne biki na 9 da ke cikin bukukuwan yanayin sararin samaniya 24. Mai yiyuwa ne ranar bikin ta kan zo a ranar 5 ko ranar 6 ko ranar 7 ga watan Yuni a kowace shekara. Game da kalmar "Mang" cikin Sinanci, ma'anarta ita ce kayar zangarnun alkama da sauran irinsu, a wurin nan, an nuna cewa, lokacin ya yi da za a girbi shuke-shuken da ke da kayar zangarnu, kamar su alkama da sauran irinsu, Kalmar "Zhong" da ke cikin Sinanci ma'anarta ita ce, shuka shuke-shuke a gonaki ke nan, a wurin, an nuna cewa, lokacin ya yi da za a shuka masara da dawa da gero da suaran irinsu, shi ya sa bikin "Mangzhong" ya alamanta lokacin ya yi da za a soma girbi shuke-shuken da ke da kayar zangarnu da sauran irinsu da kuma lokacin ya yi da za a soma shuka shuke-shuke kamar su masara da sauran irinsu.

A yawancin wuraren kasar Sin, musamman ma a arewacin kasar Sin, lokacin bikin Mangzhong ya soma zuwa, sai an soma girbi amfanin gona da suke nuna a yanayin zafi, sa'anan kuma za a shuka shuke-shuken da za su nuna a yanayin kaka, sa'anan kuma za a mai da hankali ga kula da masara da dawa da gero da sauran shuke-shuken da aka shuka su a yanayin bazara, lokacin nan, ana girbi, ana yin shuke-shuke, kuma ana kulawa da shuke-shuke bi da bi, lokacin nan lokaci ne da aka samu ayyuka mafi yawa. Saboda haka, a wajen jama'a, manoma suna kan kira bikin "Mangzhong" da cewar wai ayyukan da yawa ne da ake yin namijin kokari wajen shuka shuke-shuke a gonaki. Akwai wani karin magana na kasar Sin da cewa, girbin alkama tamkar ceton gobara, da kuma kwace hatsi daga bakin Dragon. Wannan karin magana ya bayyana sosai cewa, ya kamata a yi kokarin shiga aikin girbe-girbe da kuma jigirarsu cikin gaggawa da raba tsabar daga soshiyar hatsi. Akwai wani karin magana daban da cewa, bai kamata ba a bata yini daya wajen aikin noma a yanayin bazara, amma a yanayin zafi, bai kamata ba a bata awa daya. Fasahohin da manoma suka samu da kuma gwaje-gwaje da yawa da aka yi ta hanyar kimiyya dukkansu sun shaida cewa, ba za a iya samun girbi mai armahi ba in an jinkirtar da lokacin shuka shuke-shuke.

Kasar Sin tana da makekiyar kasa, saboda haka shiyyar arewacin kasar da kudancinta na da bambanci sosai. A wannan lokaci, shiyyar kudancin kasar Sin ta shiga lokacin yanayin damuna , mai yiyuwa ne ana ruwan sama har cikin wata guda, a lokacin, saboda wasu 'ya'yan itatuwa kamar dinya sun nuna, shi ya sa ana kiran yanayin da cewar wai yanayin ruwan sama da dinya ke nuna. A wannan lokaci, ana samun ruwan sama da yawa, amma ba a sami hasken rana da yawa , wani lokaci ma ana samun dan sanyi.

Sa'anan kuma, a wajen manoma masu noman shayin ti na kasar Sin, yanayin "Mangzhong" shi ma yanayi ne mai muhimmanci gare su, kuma biki mai muhimmanci ne gare su. Shayin ti na kasar Sin na da banbanci sosai wajen lokutan cire su, wato akwai wasu da aka cire su a yanayin bazara, wasunsu da a kan cire su a yanayin zafi da wasunsu ana cire su a yanayin kaka, in lokacin Mangzhog ya zo, yawancin manoma masu noma shayin ti suna cire ganyayen ti ba tare da bata lokaci ba, duk saboda zafi ya zo, ganyaye suna girma da sauri, in ba a cire su cikin gaggawa ba, to ganyayen ti za su tsoffa, wannan zai kawo mugun tasiri ga ingancin shayin ti da dadinsa.(Halima)