Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 19:39:00    
Gasar wasannin Olympic ta kusanci ga kasar Sin

cri
Yanzu bari mu koma zuwa ran 29 ga watan Yuli na shekarar 1952, wato a yayin da kasar Sin ta kafu ba da dadewa ba, kungiyar 'yan wasan Olympic da kasar Sin ta tura ta halarci bikin daga tuta a kauyen 'yan wasa da suka shiga gasar wasannin Olympic ta karo na 15 a birnin Helsinki na kasar Finland. Wannan shi ne karo na farko da sabuwar kasar Sin ta bulla a gun gasar wasannin Olympic. Sabuwar kasar Sin ta jure wahalhalu da yawa domin shiga gasar wasannin Olympic a karo na 15.

A sakamakon cikas da wasu kungiyoyi na kasashen duniya suka kawo mata, a dai dai ranar kafin budewar gasar wasannin Olympic ta karo na 15, kasar Sin ta sami gayyatar shiga gasar wasannin Olympic din nan. Baya ga cikas daga waje, sabuwar kasar Sin ta kuma fuskanci matsalar tattalin arziki a gida. Ko da yake kasar Sin ta fuskanci matsalolin karancin lokaci da kuma karancin karfi, amma ta kafa wata kungiya mai mambobi 40 cikin gajeren lokaci, wadda ta je Helsinki ba dare ba rana. A yayin da kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin ta sauka Helsinki, ya rage sauran kwanaki 5 kawai da rufe gasar wasannin Olympic. Dukkan kungiyoyin wasan kwallon kafa da wasan kwallon kwando na kasar Sin sun rasa gasannin share fage , sai dan wasan ninkaya Wu Chuanyu kawai ya sami damar shiga gasar share fage ta ninkayar rigingine na mita 100.

Don me sabuwar kasar Sin ta nace ga shiga gasar wasannin Olympic? Rong Gaotang, shugaban kungiyar 'yan wasan kasar Sin ya ba da amsa kamar haka a gun bikin daga tuta a kauyen wasannin Olympic, ya ce, 'ko da yake mun makara, amma a karshe dai mun zo nan tare da kyakkyawan fatan alheri kan samun zaman lafiya da kuma zumunci.'

Amma duk da haka, a sakamakon kayyadewa daga kasashen duniya a wancan lokaci, sabuwar kasar Sin ta bulla a gun gasar wasannin Olympic ta Helsinki a shekarar 1952 cikin gajere lokaci, daga baya, ta dakatar da shiga wannan muhimmiyar gasa har shekaru 32. Shahararren masani Mr. Qin Xiaoying yana ganin cewa, wannan shi ne asarar da kasar Sin ta samu, haka kuma, shi ne asarar da wasannin Olympic suka samu. Mr. Qin ya ce,'Babu tamtama, kasashen duniya sun yi babbar asara, saboda a lokacin can kasar Sin tana da mutane fiye da mililyan 600, in mutanen Sin ba su shiga gasar wasannin Olympic ba, to, an yi babbar asara wajen raya wasannin Olympic. '

A shekarar 1984, wato bayan shekaru 32, kasar Sin ta sake bullowa a kan dandamalin wasannin Olympic. An yi gasar wasannin Olympic ta karo na 23 a birnin Los Angeles ne a cikin muhallin duniya mai yamutsi kamar yadda aka taba fuskanta a da. Wani mashahuren kwararre dabam wato Tao Wenzhao ya yi nazari da cewa,'An shirya gasar wasannin Olympic ta Los Angeles a cikin halin musamman. A lokacin can, tsohuwar kasar tarayyar Soviet da wasu kasashen gabashin Turai sun kaurace wa gasar wasannin Olympic ta Los Angeles, in kasar Sin ita ma ba ta shiga ba, to, gasar wasannin Olympic ta Los Angeles za ta fuskanci hali mai ban kunya.'

A shekaru 1970, kasashen Sin da Amurka sun yi amfani da damar shirya gasar wasan kwallon tebur a tsakaninsu a matsayin harkokin jakadanci, sun kulla huldar jakadanci a tsakaninsu a shekarar 1979 a hukunce. Huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta sami kyautatuwa sosai. Peter Uberroth, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Los Angeles na lokacin can ya sifanta mana halin da yake ciki a lokacin da ya san cewa, kasar Sin za ta aika da kungiyar 'yan wasa domin shiga gasar wasannin Olympic, ya ce,'Manzon da muka tura zuwa Beijing ya gaya mini cewa, Mr. Uberroth, kasar Sin ta tabbatar da cewa, za ta shiga gasar wasannin Olympic! '

A gun gasar wasannin Olympic da aka yi a Los Angeles, an yi maraba da kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin da hannu biyu biyu kuma bisa babban matsayi. A yayin da kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin ta bulla a gun bikin budewa gasar, dukkan 'yan kallo fiye da dubu 90 sun yi ban tafi a tsaye. Sa'an nan kuma, bangaren Amurka ya sanya kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin ta zama ta farko da ta daga tuta a kauyen wasannin Olympic.

A cikin awoyi 24 da bude gasar wasannin Olympic ta Los Angeles, dan wasan harbe-harbe Xu Haifeng na kasar Sin ya sami lambar zinariya a cikin gasar harbe-harbe da libarba a tsakanin maza, wadda lambar zinariya ce ta farko a gun wannan gasar wasannin Olympic ta Los Angeles. Shugaba Juan Antonio Samaranch na kwamitin wasannin Olympic na duniya da kuma Mr. Uberroth, shugaban kwmaitin shirya gasar wasannin Olympic ta Los Angeles na wancan lokaci sun halarci bikin ba da lambobin yabo ga Xu Haifeng, inda Mr. Uberroth ya yi bayani ga 'yan kallo da cewa,'Ina so in tuna da ku cewa, watakila ba ku gano ba, lokacin yanzu lokaci ne mai muhimmanci a tarihi. Lambobin zinariya da tagulla za su shiga hannun 'yan wasa da suka zo daga wata kasa da ba ta taba samun lambobin yabo a cikin gasar wasannin Olympic ba.'

Amma lambar zinariya da Xu Haifeng ya samu ya kasance mafari ne kawai. A gun gasar wasannin Olympic ta Los Angeles, kasar Sin ta sami lambobin zinariya 15.

Kyakkyawar bullowar kasar Sin a cikin gasar wasannin Olympic ta karo na 23 tana da nasaba da manyan sauye-sauye da kasar Sin ta samu a gida. A lokacin can, kasar Sin ta riga ta yi shekaru 6 tana yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. Mr. Qin ya takaita mana halin da kasar Sin ke ciki a wancan lokaci. Ya ce,'A cikin wadannan shekaru 6 da kasar Sin take yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta fi bayar da muhimmanci kan yin gyare-gyare a kauyuka, ta haka ta karfafa gwiwar manoma kusan miliyan 700 a kasar Sin. Hatsin da aka samu daga karshen shekarar 1983 da ta 1984 ya biya bukatun dukkan Sinawa, wannan shi ne karo na farko da dukkan mutanen Sin suka sami isasshen abinci. Sa'an nan kuma, a lokacin can, kasar Sin ta shiga mataki na yin gyare-gyare kan wasannin motsa jiki da ba da ilmi da al'ada da kiwon lafiya da kimiyya da fasaha daga dukkan fannoni.'

A lokacin da kasar Sin take yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje, mutanen Sin sun canza ra'ayoyinsu da kuma tunaninsu kan wasannin Olympic da kuma duniya. A ran 24 ga watan Satumba na shekarar 1993, ko da yake birnin Beijing bai sami bakuncin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2000 bisa kuri'u 2 kawai ba, amma mutanen Sin sun iya fuskantar wannan sakamako cikin natsuwa.

A lokacin da muke waiwaya tarihi, mun gano cewa, ko da yake Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun tsoma baki cikin neman samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic da kasar Sin ta yi a shekarar 1993, amma mutanen Sin sun kusanci wasannin Olumpic, ba su daina kusantar da kansu ga duniya ba.

A lokacin bazara na shekarar 1992, Deng Xiaoping, babban mai zayyana manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin ya jaddada cewa, samun bunkasuwa yana gaba da kome. Ya kuma karfafa gwiwar mutane da su yi gyare-gyare da kuma kirkire-kirkire ba tare da jin tsoron kome ba, ta haka kasar Sin ta shiga sabon mataki na yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. Tun daga shekarar 1993 da kasar Sin ta ci turar samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic, har zuwa shiga sabon karni da kasar Sin ta ci gaba da neman samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic, mutanen Sin sun kara yin farin ciki bisa shiga ayyukan neman samun bakuncin gasar wasannin Olympic, haka kuma, sun kara nuna sha'awa kan shiga gasar wasannin Olympic.(Tasallah)