Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-01 20:21:11    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, "Kungiyar al'adu ta Gaojinsumei" da ke hade da 'yan kananan kabilu fiye da 100 na yankin Taiwan sun tashi daga birnin Taibei kuma sun iso nan birnin Beijing ta jirgin saman shata wanda yake zirga-zirga tsakanin gabobi 2 na zirin tekun Taiwan a kowanen karshen mako, sun zo nan ne musamman domin nuna wasanni kafin lokacin bikin bude wasannin Olimpic da za a yi a ran 8 ga wata mai zuwa.

Bisa labarin da aka bayar an ce, yawancin mambobin "Kungiyar al'adu ta Gaojinsumei" ba 'yan wasa na sana'a ba. Tsawon lokacin wasannin da wadannan 'yan kananan kabilu za su nuna a gabannin bude wasannin Olimpic na Baijing ya kai kusan minti 3 da dakika 40, daga cikin wasannin da za su nuna har da wakokin gargajiya na musamman da 'yan kabilar Bunong za su rera, da irin rawa mai sigar musamman da 'yan kabilar Pinan za su yi, da kuma "Rawar Gashi" da 'yan kabilar Dawu dake tsibirin Lanyu za su yi.

---- Kwanan baya, an bude sabon babban dakin kimiyya da fasaha na jihar Xinjiang ta kasar Sin a hukunce, wannan babban daki zai ba da taimako wajen yada kimiyya da kara samun wayewar kai har a zuci, sa'an nan kuma zai zama tashar aiki da ma'aikatan cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin suka kafa a jihar Xinjiang domin ba da shawarwari kan harkokin kimiyya, sabo da haka za a aza harsashi mai karfi wajen kafa sabon tsarin hadin gwiwa a tsakanin ma'aikatan cibiyar da jihar Xinjiang.

Mr. Nur Bekri, shugaban jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, domin kara shigar da samari da yara mafi yawa cikin dakin kimiyya da fasaha domin kadakar da kansu wajen kimiyya da kara kwarewarsu wajen aiki, da yin horo da tallafa sabbin kwararru da yawa, jihar Xinjiang ta shafe shekaru 3 tana gina wannan babban dakin kimiyya da fasaha na zamani wanda ke amfani wajen barbaza kimiyya da yin mu'amalar ilmi da horas da mutane wajen kimiyya da fasaha, wannan ya zama sabon sakamakon da jihar Xinjiang ta samu wajen bunkasa harkokin kimiyya da fasaha cikin shekaru 30 da suka wuce kuma bisa manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Wannan sabon babban dakin kimiyya da fasaha fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 13.6, muhimmin gininsa yana da hawa 10.