Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-01 16:15:27    
'Yan wasa nakasassu na Afirka ta kudu na fatan samun kyawawan nasarori a Beijing

cri

Ko da yake tawagar 'yan wasan Afirka ta kudu ba ta sami sakamako mai kyau sosai ba a gun wasannin Olympic na Beijing, inda suka ci lambar azurfa daya kawai, amma duk da haka, wannan bai sauyaya gwiwar 'yan Afirka ta kudu ga wasannin Olympic ba. A halin yanzu dai, suna fatan 'yan wasansu nakasassu da za su tashi zuwa wajen wasannin Olympic na nakasassu da za a fara yi a birnin Beijing za su sami kyawawan nasarori.

A ran 28 ga wata da dare, an gudanar da kasaitaccen biki a birnin Johannesburg domin tawagar 'yan wasa nakasassu da za su tashi zuwa birnin Beijing. Tawagar na kunshe da mutane 123, wadanda suka hada da 'yan wasa 60, ciki kuma har da Natalie du Toit, shahararriyar 'yar wasan iyo, wadda ta shiga gasa da 'yan wasa da ba nakasassu ba a gun wasannin Olympic na Beijing, da kuma Oscar Pistorius, shahararren dan wasan gudun gajeren zango na kasar.

A gun wasannin Olympic na nakasassu da aka yi a birnin Athens, tawagar 'yan wasa nakasassu ta Afirka ta kudu ta sami lambobin zinari 15 tare da na azurfa 13 da kuma na tagulla 8. A gun wasannin Olympic na nakasassu da za a yi wannan karo kuma, za su yi kokarin neman cin lambobi a fannoni 8.

Mr.Moss Mashishi, shugaban kwamitin wasannin Olympic na Afirka ta kudu, wanda ya koma daga birnin Beijing tare da tawagar 'yan wasan Afirka ta kudu, ya ce, ko da yake sabo da dalilai da yawa ne, tawagar 'yan wasan Afirka ta kudu ba ta sami kyawawan nasarori sosai ba, amma duk da haka, jama'ar Afirka ta kudu ba su daina bin tunanin wasannin Olympic ba. Mr.Mashishi bai bayyana makasudin da tawagar 'yan wasa nakasassu ya Afirka ta kudu ke neman cimmawa a gun wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ba, amma ya ce, 'yan wasan Afirka ta kudu za su ci gaba da yin iyakacin kokarinsu wajen neman samun kyawawan nasarori.

A sa'i daya kuma, Mr.Mashishi ya nuna babban yabo ga yadda aka gudanar da wasannin Olympic a birnin Beijing, ya ce yana nuna cikakkiyar amincewa ga bayanin shugaba Jacques Rogge na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa a kan wasannin Olympic na Beijing, wato "wasannin Olympic ne mai kyau da ba safai a kan ga irinsa ba", sabo da gaskiya ne Sin ta yi gaggarumin aiki.

Oscar Pistorius, shahararren dan wasan gudun gajeren zango na Afirka ta kudu, ya ce, zai shiga gudu mai tsawon mita 100 da na mita 200 da kuma na mita 400 a gun wasannin Olympic na nakasassu da za a yi a birnin Beijing. A gun wasannin Olympic na nakasassu da aka yi a birnin Athens a shekarar 2004, Pistorius ya taba samun lambar zinari a gudun mita 200, sa'an nan, ya sami lambar tagulla a gudun mita 100.

Natalie du Toit, wadda ba da jimawa ba ta kammala gasa a gun wasannin Olympic na Beijing, kuma a halin yanzu ke cigaba da kasancewa cikin birnin, ta taba samun lambobin zinari 5 tare da ta azurfa daya a gun wasannin Olympic na nakasassu na Athens, kuma ana sa ran za ta cigaba da samun nasarori a gun wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.

Mataimakiyar shugaban Afirka ta kudu, Madam Phumzile Mlambo-Ngcuka, wadda ta je wajen bikin takanas domin ban kwana da tawagar 'yan wasan kasar, ta ce, Sin ta riga ta gudanar da wasannin Olympic mai annashuwa ga duniya, kuma tabbas ne za ta gudanar da wasannin Olympic na nakasassu mai kyau daidai kamar wasannin Olympic da ta gudanar, kuma cike take da imani. Tana kuma fatan 'yan wasa nakasassu na Afirka ta kudu za su shiga wasanni hankali a kwance, ko wane sakamako ne suka samu, gwamnatin Afirka ta kudu da jama'arta za su nuna musu goyon baya har abada.(Lubabatu)