Ran 27 ga wata da dare, a cikin filin jirgin sama na Yata da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya, mutane da yawa sun taru gu daya, inda suka yi kide-kide da raye-raye domin yin maraba da 'yan wasan kasar Kenya da suka komo gida bayan da suka halarci gasar Olympic ta Beijing tare da nasara. Yanzu ga labarin da wakilnmu Mr. Wei Tong ya ruwaito mana daga filin jirgin saman na kasar Kenya.
'Dan wasan kasar Kenya BUNGEI Wilfred wanda ya samu lambar zinariya cikin gasar gudu ta mita 800 ta maza ya fito daga filin jirgin sama da farko. Iyalansa da abokansa sun ba shi madara ta hanyar musamman na kabilar Kalenjin. Mr. Bungei ya shanye madara kuma yana jin zumudi sosai, ya sha fadin cewa, "ni ne mutum mafi jin dadi a duniya". Ya ce, "Yayin da nake wuce layin karshe, ban san na zama na farko ba. Ina yin tambaya da kaina cewa, Allah, ko ni ne zakara? Saboda ana yin gasa mai tsanani, wasu 'yan wasa suna da karfin yin takara sosai, sun taba wuce ni cikin gasa. Yayin da muke kai layin karshe, wasu 'yan wasan da ke cikinmu sun wuce layin karshe kamar a lokaci daya. Daga baya, na san na sami lambar zinariya, a lokacin can, ina jin farin ciki kamar na ci lambar yabo ta Nobel, yanzu ni ne mutum mafi jin dadi a duniya."
Mr. Musyoka mataimakin shugaban kasar Kenya ya zo filin jirgin sama da kansa domin yin maraba da 'yan wasa. Ya taya su murna kan lambobin yabo da suka samu, kuma yana jin alfahari sosai a sakamakon kokarin da suka yi cikin gasanni. Ya ce, ba mutanen da suka samu lambobin yabo kawai ba, har ma 'yan wasan wadanda ba su samu lambobi ba, ina son taya su murna gaba daya.
"Nasarorin da kuka samu, nasarar kasar Kenya, kuma ina so na gaya muku, dukkan ku wadanda suka samu lambobin yabo, ko wadanda ba su samu ba, kuna yin kokari sosai, kuma ina jin alfahari gareku, saboda kun shiga gasanni. Ban da haka kuma, a ciikin gasannin Olympic ta Beijing, dukkanku 'yan kasar Kenya ne."
Mataimakin Musyoka ya nuna cewa, abin kawatar da ni a birnin Beijing shi ne jarabar jama'ar kasar Sin. A sa'i daya kuma, ya yaba nasarorin da 'yan kasar Sin suka samu kwarai. Yana fatan kasar Kenya za ta yi koyi da kasar Sin, da kara zuba jari kan sha'anin motsa jiki, da cigaba da inganta karfin kasar Kenya kan fannin motsa jiki, ta haka za a cimma burinta na zama wata kasa mai karfin motsa jiki a Afirka. Mr. Musyoka ya ce, "Za mu cigaba da zuba jari da kayayyaki kan sha'anin motsa jiki, da rike matsayin rinjaye na kasar Kenya. Kuma za mu koyar da 'yan wasa na kwallon kafa, da na kwallon volleyball. A sa'i daya kuma, za mu yi hayar malaman koyar da wasan lankwashe jiki na kasar Sin domin horar da 'yan wasan kasar Kenya. Ya kamata mu yi koyi da kasar Sin, nan gaba za mu yi kokari domin bunkasa sha'anin motsa jiki, ta haka domin kara karfin kasar Kenya kan fannin tattalin arziki."
A cikin gasar Olympic ta Beijing, kungiyar 'yan wasan kasar Kenya ta samu kyakkyawan sakamako. Gaba daya ta samu lambobin yabo 14, wato lambobin zinariya 5, da azurfa 5 da tagulla guda 4, kasar Kenya tana kan matsayi na 15 cikin jerin sunayen kasashen da suka samu lambobin yabo, ta zama kasa ta farko cikin kasashen Afirka, kuma ta samu lambobin yabo na gasar Olympic mafi yawa cikin tarihin kasar Kenya.
|