Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-29 17:35:13    
Kasar Sin ta kafa dokoki domin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki irin na bola jari

cri

A yayin da kafofin watsa labaru sun yaba wa kauyen Olympics na Beijing wajen sake yin amfani da shara, domin kara sa kaimi ga canzawar bunkasuwar tattalin arziki, a ran 29 ga wata, kasar Sin ta fitar da wata muhimmiyar doka wato dokar sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki irin na bola jari. Wata ma'ana da ta fi muhimmanci ta wannan doka ga jama'ar kasar Sin, da kasuwanni, da kamfanoni, da kuma gwamnati ita ce, an mayar da tattalin arziki irin na bola jari daga ra'ayi zuwa wani hakikanin abu.

A wa'adin farko na yunkurin kafa dokar sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki irin na bola jari a shekarar bara, da aka tabo magana kan muhimmiyar ma'ana ta wannan doka, kwararren tattalin arziki na kasar Sin Mr. Feng Zhijun ya bayyana cewa,

'Abu na farko wajen bunkasa tattalin arziki irin na bola jari shi ne domin samar da sabon makamashi ga bunkasuwar tattalin arziki. Abu na biyu shi ne, domin rage yawan kayayyakin da suke iya gurbata muhalli. Abu na uku shi ne, domin kara ingancin tattalin arziki.'

A ganin Mr. Feng, wannan doka kuma ta yi la'akari kan hakikanin halin da kasar Sin take ciki, da kuma bukatar kasar Sin. Ya ce,

'Kasashe masu sukuni na yamma sun fi mai da hankulansu kan yadda ake sake yin amfani da shara a yayin da suke bunkasa tattalin arziki irin na bola jari, amma kasar Sin tana cikin wa'adin masana'antar da kasa cikin sauri. Sabo da haka ne, kamata ya yi mu mai da hankali kan yadda ake kara ingancin makamashi da tsimin makamashi.'

Za a fara yin amfani da dokar sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki irin na bola jari daga farkon shekara mai zuwa, a halin yanzu dai, gwamnatin kasar Sin tana shirin yin gyare gyare kan ma'aunai da yawansu ya kai 300 da abin ya shafa. Game da haka, tsohon darektan babbar hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasar Sin Mr. Li Chuanqing ya bayyana cewa,

'Game da ayyukan share fage na dokoki, majalisar gudanarwa ta kasar Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa sun tsara wasu ka'idoji, kamar shirin bunkasa tattalin arziki irin na bola jari, da hanyoyin da ake bi domin sa ido kan manyan kamfanoni da suke fi yin amfani da ruwa da dai sauransu, wadannan ka'idoji kuma za su ba da taimako wajen gudanar da dokar sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki irin na bola jari.'(Danladi)