Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka san cewa, a yanzu haka dai, ana nan ana gudanar gagarumar gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. Amma ko kuna sane cewa, tuni wassu kafofin yada labaru na kasashen duniya, musamman ma jaridun ketare da ake bugawa cikin harshen Sinanci sun kebe shafunansu na musamman domin bayar da labarai a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 yayin da suke nuna kyakkyawan fatan alheri ga wannan gagarumar gasa a madadin Sinawa da kuma Sinawa 'yan kaka-gida dake wurare daban-daban na duniya..
Jaridar " Zhonghua Daobao" ta kasar Canada na daya daga cikin jaridun da suke yin kaurin suna cikin jama'ar wurin ta taba samun lambar yabo mafi kyau ta kafar yada labarai da harshen Sinanci daga gwamnatin Canada a shekarar 2006. Wannan jarida ta kebe wani shafin musamman don buga labarai dangane da gasar wasannin Olympics ta Beijing; Ban da wannan kuma ta fito da bayanin musamman a ranar 8 ga wannan watan da muke ciki domin tunawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Babbar editan jaridar din mai suna Bei Ren-ren ta fada wa wakilinmu cewa: " Aminai masu sauraron gidan rediyon kasar Sin wato CRI, sannunku! Ni ce babbar editan jaridar ' Zhonghua Daobao'. A yanzu haka dai, dukkan Sinawa dake zaune a kasashen waje suna zura ido kan gasar wasannin Olympics ta Beijing da ake gudanarwa yayin da suke taya murnar samun wannan lokaci mai sosa ran mutane ta hanyoyi daban-daban. Muna fatan dukkan Sinawa za su yi alfahari domin kasar mahaifarmu yayin da muke bada taimako gare ta a sana'o'I daban-daban.''
Jama'a, ko kuna sane da cewa, a birnin Brisbane, hedkwatar jihar Queensland ta kasar Australiya, akwai Sinawa sama da 100,000 dake zaune a can, inda kuma akwai jaridar " Yimin Jingbao" ta yankin Australiya da ake buga cikin harshen Sinanci,wadda kuma ta fi yin tasiri ga wurin. Babban editan jaridar nan mai suna Lang Jingchao ya yi farin ciki da fada wa wakilinmu cewa: " Mun rigaya mun kebe shafuna biyar na musamman domin buga labarai a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing. A lokaci guda, za mu yi hadin gwiwa sosai tare da gidan rediyon CRI wajen bayar da labarai masu ban sha'awa kuma cikin lokaci ga masu karanta jaridar."
Sa'annan Mista Lang Jingchao ya furta cewa, da yake a karon farko ne ake gudanar da gasar wasannin Olympics a kasar Sin, shi ya sa Sinawa dake zaune a yankin Australiya dukkansu suna lura da wannan gagarumar gasa. Alal misali: sun gudanar da jerin bukukuwan nuna wasannin fasaha domin marabtar gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Jama'a, yanzu dai zan dan gutsura muku yadda wassu jaridu da mujalloli na kasar Amurka suka kebe shafunan musamman don bayar da labarai kan gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Kwanan baya bada dadewa ba, jaridar da ake kira " Washington Post" ta kebe wani layi gaba daya a cikin shafinta na farko da aka rubuta babbakun Sinanci masu launin ja a kai a kan cewa " Gasar Wasannin Olympics ta Beijing". An bayar da labarin cewa, kungiyar 'yan wasan kasar Sin tana kan matsayin rinjaye a fannin wasan kwallon tebur, da wasan tsunduma cikin ruwa da wasan lankwashe-lankwashen jiki wato Gymnestics da kuma wasan tseren kwale-kwale da dai sauran fannoni.
Ban da wannan kuma, mujallar mako-mako da ake kira " Time" ta buga wani bayani a shafinta na farko, inda aka bayyana 'yan wasa 100 da suka cancanci a zura ido a kansu. Kuma 'yan wasa guda 5 dake kan gaba a sahun wadannan 'yan wasan su ne: Lebran James, dan wasan kwallon kwando a NBA, da shahararrun 'yan wasan iyo su Dara Torres da Michael Phelpe, da kuma 'yan wasa na kasar Sin wato Liu Xiang da Yao Ming.
Dadin dadawa, jaridu da mujalloli iri daban-daban na kasar Amurka sun buga wassu gajerun labarai domin dan gutsura wa masu karantawa gasar wasannin Olympics ta Beijing, kamar tambarin gasar wasannin, da kayan kawo wa mutane gamon katar, da lambobin yabo na wasannin da kuma gine-ginen wasannin kamar na "Bird's Nest" da na " Water Cube" da dai sauransu.( Sani Wang)
|