Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 15:38:13    
Manzanni masu kiyaye lafiya da harsuna (babi na biyu)

cri

"Barka da zuwa! Nan cibiyar ba da agajin gaggawa ta asibitin birnin Beijing mai wayar lamba 120, ko kana bukatar wani taimako? Ko kana bukatar motar ba da agajin gaggawa ta asibiti, a shirye muke za mu tura motar,sai ka yi hakuri ka yi jira, mene ne kake fama da shi?"

Maganar da kuka ji dazu,Magana ce da mallama Luo Xiaojing,'yar sa kai da ke iya Magana da harshen Spanish ta yi yayin da ta ke cikin shirin aiki a cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing mai wayar lamba 120, tana Magana da wani mutum da ya shiga burtun bakon spain wanda yake neman taimako.

Da aka fara wasannin Olympics a birnin Beijing ana bukatar kwararru masu iya Magana da harsuna da yawa na kasashen waje. Tun daga karshen shekara ta 2006 ne cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing mai wayar lamba 120 ta fara daukar mutane masu iya Magana da harsunan waje duk domin bad a hidima ga baki masu yawon shakatawa da 'yan wasa na kasashen waje yayin da ake yin wasannin Olympics a nan birnin Beijing.wadannan mutanen da aka dauka dukkansu masu aikin sa kai ne. Bisa jagorancin da likitocin cibiyar suka yi musu,ma'aikata masu sa kai sun yi atisayen ayyukan ba da agajin gaggawa,kamar su amsa wayoyin neman taima da baki, da yi mu'amala da su da kuma biya bukatunsu,sun kuma ba da taimakonsu ga likitocin cibiyar wajen ayyukan yau da kullum.

Malama Luo Xiaojing tana daya daga cikin ma'aikata masu sa kai dake iya Magana da harsunan waje da cibiyar bad a agajin gaggawa ta birnin Beijing ta dauka, aikinta shi ne amsa wayoyi da mutane masu yaren Spain dake neman taimako za su yi a lokacin wasannin Olympics a nan birnin Beijing. Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta shiga aikin sa kai a cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing, malama Luo Xiaojing ta bayyana cewa" bayan da na kammala karatuna a jami'a ina aiki a ma'aikatun kiwon lafiya, na yi aiki tare da likitoci cikin shekaru uku a kasashen waje, wasu kalmomin da ake amfani da su a fannin likitanci ko na sinanci ko na spainish na saba da su, ina tsammani babu matsala gare ni wajen amsa wayoyin baki. Zan iya sauke nauyin da ke bisa wuyana da kwarewata a harshen Spain.

A kan matsayin dan sa kai,wani dalibin dake koyon harshen Japananci a jami'ar koyon harsunan waje ta biyu ta birnin Beijing mai suna Sun Peng yana mai ra'ayin cewa amsa wayoyin neman taimako a cibiyar ba da taimakon gaggawa ta birnin Beijing mai wayarlamba 120 ba aiki mai sauki ban e,ba ma kawai yana bukatar ka kware a harshe ba har ma ya kamata kana da wasu ilimi game da likitanci,babbar jarabawa gare ni.ya ce ya niyyata zai dauki wannan nauyi.Ya ce "wasannin Olympics na shekara ta 2008,wata muhimmiyar dam ace. A hakika ina so in shiga dukkan ayyukan sa kai. Ayyukan ba da taimakon gaggawa na cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120 wani batu ne mai muhimmancin gasket, a ganina shiga ayyukan sa kai tana da amfani sosai, na iya taimaka mutane masu Karin yawa."

Da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya duba takardun sunayen, ya ga shekarunsu sun sha banban,, yayin day a ke Magana da su,ya ga ko kwararru tsofaffi ko samari masu kuruciya,dukkansu sun bayyana burinsu na shiga ayyukan sa kai da ba da taimakonsu ga wasannin Olympics na Beijing.

Bisa labarin da muka samu, an ce a lokacin yin wasannin Olympics a nan birnin Beijing da akwai mutane masu asalin kasashen ketare da suke so su ba da taimako, cibiyar bad a agajin gaggawa mai wayar lamba 120 ta yi shiri sosai a wannan fanni.Madam Wang Xuehong, likita direkata ta cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120 ta birnin Beijing ta bayyana cewa an yi shiri sosai a fannoni uku. " mun yi wa ma'aikatamu masu aikin tsara shire shiryen ayyuka horo,mun tura su cikin jami'ar koyon harsuna ta birnin Beijing don samu horo rukuni bisa rukuni.na biyu tun karshen watan Disamba na shekara ta 2006, mun fara daukar ma'aikata masu sa kai da ke iya harsunan waje. Ban da wannan kuma mun baiwa wadanan masu sa kai horo kan ba da taimakon gaggawa a fannin asibiti cikin rukunoni biyu. Madam Luo Xiaojing ta shiga kos da aka shirya a watan Mayu domin zabar ma'aikata masu sa kai.Wannan kos ya ba ta alamu masu kyau a cikin zuciyarta,ta waiwayo yadda aka yi mata horo. Ta ce bayan da aka ba mu horo,aka baiwa kowanenmu kasidu guda biyu, daya daga cikinsu kasida ce mai kunshe da ilimin likitanci,wata dabam kuwa ta bayar da ilimi kan yadda ake yin ayyuka a cibiyar kuma yadda aka ba da taimakon gaggawa.A cikin kasida daban an kuma bayyana ka'idojin da ake bi wajen ba da taimakon gaggawa a cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120, har ma da akwai maganganu da akan amfani da su cikin harsuna guda tara kan aikin ba da agajin gaggawa. A cikin kasidu an kuma bayar da misalai kan cututtukan da aka gani kullum da hadarori da masifu da kuma matakan da ya kamata a dauka,da ilimi game da baiwa juna taimakon da ake bukata ba tare da bata lokaci ba.

Mr Bai Jixing,wani tsoho mai aikin sa kai da harshen turanci ya zo ne daga wani kamfanin kula da kayayyakin fasaha na fici da shigi na kasar Sin ya kuma kawo shawarwari ga sassan da abin day a shafa inda y ace kamata ya yi a ba kowane wuri suna daya cikin turanci,kada a kuskura ko a shiga duhu saboda fassara da aka yi bai zo na daya ba cikin turanci.

Mr Bai Jixing y ace a ganina lokaci yana da muhimmanci sosai wajen bad a agajin gaggawa a cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120. idan ka makara da awa daya kana binciken inda baki ke sauka,lalle a sami babbar matsala. Shi ya san a kawo shawarar kamata ya yi a shirya duk takardun da ake bukata a cibiyar, idan wani bako ya buga mana waya,ya kamata mu san inda yake nan da nan,mun iya ba shi labarin da yake bukata, mun tura motar ambulance tare da likitoci zuwa wurinsa ba tare da bata lokaci ba."

Duk lokacin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya ke Magana da ma'aikata masu sa kai,sun yi farin ciki da jin dadin aikin da suke yi. Himma da imanin da suka nuna sun girgiza kawunanmu. Da yak e ma'aikata masu sa kai sun kasha lokaci mai tsawo wajen yin ayyukansu,sun samu goyon baya daga iyalansu. Matar Mr Bai Jixing Madam Wang Yuying ta bayyana cewa  "mijina yak ware wajen harshen ketare,ya iya taka muhimmiyar rawa. A duk lokacin da ake bukatar taimako daga sauran mutane musamman baki,ya iya bad a taimakonsa ga wadanda suke bukata.yanzu lokaci ya yi da ake yin wasannin Olympics a nan birnin Beijing,baki masu yawa daga sauran kasashen duniya sun zo nan kasar Sin,ya kamata mu tafiyar da kome yadda ya kamata a dukkan fannoni mu ba su taimako. Ina goyon bayan mijina da ya dauki nauyi a wannan fanni."

Wani dalibi na kasar Turkey da ya ke karatu a nan kasar Sin mai suna Alijiang ya jiku da ya samu labarin bude cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120 a lokacin wasannin Olympics na Beijing ya ce "wayar mai lamba 120 a kasar Sin kamar wayar mai lamba 112 ko wayar 911 a wasu kasashen yamma, cibiyar mai wayar lamba 120 za ta iya ba da taimakon gaggawa a fanning asibiti ga 'yan kallo da 'yan wasa na kasashen waje cikin lokaci,lalle hidima ce mai amfani da ya wajaba da ake bayarwa. 'Yan kallo da yan wasa na kasashen waje za su itya shiga harkokin wasannin Olympics na Beijing tare da samun tabbacin lafiyarsu a kasar Sin yayin da ake tafiyar da wasannin Olympics.(Ali)