Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 17:46:40    
Kasashe masu tasowa suna kokarin kara hasken alamar hada zobba 5 na wasannin Olimpic

cri
A gun bikin bude wasannin Olimpic na Beijing, alamar hada zobba guda 5 na wasannin Olimpic da ke alamanta manyan nahiyoyi 5 na duniya ya tashi a sararin sama na filin wasan motsa jiki na kasa mai siffar sheka, wannan kuma ya ba da alama mai ma'anar tarihi cewa, hasken alamar hada zobba 5 yana hasakaka yankunan kasar Sin, kasa mai tasowa kuma mafi girma ta duniya, kuma kasashe masu tasowa wadanda suka dauki muhimmin matsayi cikin manyan nahiyoyi 5 na duniya sun kago al'ajaba daya bayan daya a kan filayen gasar wasannin Olimpic na Beijing, sun fara morewa darajar lambobin yabo na wasannin Olimpic, halin da ake ciki a dandalin wasannin motsa jiki na duniya shi ma yana sauyawa mai faranta ran mutane.

A gun babban bikin rufe gasar wasannin Olimpic ta Beijing da aka yi ran 24 ga wata, an yi bikin rarraba lambobin yabo ga 'yan wasa masu yin gasar gudun dogon zango wato Marathon. 'Yan wasa 3 da suka zo daga Afirka ciki har da Samuel Kamau Wansiru sun hau kan dandalin samun lambobin yabo. A hakika, Afrikawa ne su fi samun nasara cikin gasannin gudun matsakaici da kuma dogon zango, ko da yake sukan tattaba wasa a zaman yau da kullum cikin halin zama mai wahalar gaske, amma wannan bai iya dakushe himmarsu wajen samun nasara ba. Tun kafin gasar, 'yar wasa Pamela Jelimo ta kasar Kenya wadda take da shekaru 19 kawai da haihuwa, wadda kuma ta samu lambar zinariya a gun gasar gudun mita 800 ta mata ta tabbatar da cewa, "Na riga na shirya sosai, na amince cewa, ba shakka zan samu nasara, kuma zan yi matukar kokari domin samun lambar zinariya domin kasar Kenya"

A gun wannan wasannin Olimpic, 'yan wasan da suka fi jawo hankulan mutane su ne na kasar Jamaika. Ko dan wasa Usain Bolt wanda ya zama zakara har sau 3, wanda kuma ya karya matsayin bajinta na duniya har sau 3, ko kuma 'yan wasa mata wadanda suka samu lambobi 3 na gaba wato suka zo ta farko da ta 2 da ta 3 cikin gasar gudun mita 100 na mata, 'yan wasan gudun gajeren zango sun tada tashen Caribbean tare da nasara, kuma sun faranta ran jama'ar Jamaika kwarai da gaske. Bayan da dan wasa Bolt ya zama zakara a gun gasar gudun mita 100 da na 200 na maza, ya yi farin ciki da cewa, "Lalle wannan abu mai girma sosai, Ni kuma ban yi tsammanin da zan iya karya matsayin bajinta na duniya har sau 2 ba, nasarar da na samu tana alamanta abubuwa da yawa gare ni."

Ban da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, kuma 'yan wasa na kasashe masu tasowa sun taka rawa mai kyau a sauran fannoni, alal misali a gun gasannin iyo, dan wasa Oussama Mellouli na kasar Tunisia ya yako nasara bisa dan wasa Grant Hackett na kasar Australiya wanda yake rike da matsayin bajinta na duniya, kuma ya zama zakara a gun gasar iyo cikin 'yanci na mita 1500 na maza, sabo da haka ya zama dan wasa Balarabe na farko wajen samun lambar zinariya a gun gasar wasannin Olimpic ta Beijing. Amma 'yar wasa Kirsty Coventry ta kasar Zimbabwe ita ma ta samu wata lambar zinariya da lambobin azurfa guda 3, tana fatan nasarar da ta samu za ta iya kara kwarin gwiwa ga 'yanuwa mutanen kasarta wajen tinkarar wahalolin da ke cikin kasar. Ta ce, "Na san dukkan mutane sun yi farin ciki kwarai, dukkansu sun yi alfahari sabo da muryar wakar mulkin kasar Zimbabwe ta tashi a wurin wasan da ake kira "water cube" wato cibiyar wasan iyo ta kasa. (Umaru)