Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 15:50:20    
Aikin share fagen wasannin Olimpic na Beijing ya samu nasara

cri

A ranar 8 ga wannan wata da safe, shugaban kwamitin wasannin Olimpic na Beijing Mr Liu Qi da shugaban kwamitin daidaituwar wasannin Olimpic na Bejing na wasannin Olimpic na duniya Mr Hein Verbruggen sun halarci bikin soma aiki da cibiyar watsa labaru ta wasannin Olimpic na Beijing.

Mun sami labari cewa, yawan manema labarun da suka yi rajista don aiki a wasannin Olimpic na Beijing ya kai 26000 ko fiye, babbar cibiyar watsa labaru ta wasannin Olimpic na Beijing da cibiyar watsa labaru ga kasa da kasa za su zama wuraren da wadannan manema labaru za su aiwatar da harkokinsu. Direktan cibiyoyin nan biyu Mr Sha Wanquan ya bayyana cewa,kafofin watsa labaru da yawansu ya kai 144 sun riga su haya dakunan ofishoshinsu 110 a cibiyoyin, wannan adadin ya kai matsayin koli a tarihin wasannin Olimpic.

Mr Hein Verbruggen ya nuna yabo sosai ga sharudan da cibiyoyin biyu suke samarwa, ya bayyana cewa, ba ma kawai babbar cibiyar watsa labaru ta zama wurin da manema labaru za su aiwatar da harkokinsu na kansu ba, har ma ta zama gidajensu na biyu, manema labaru za su aiki a wurin har cikin awo'I 24 a kowace rana, muna godiya ga wadanda suka shirya wadannan sharudan aikin, saboda sun kusan shirya wa manema labaru kome da kome da suke bukata.

****** ******** ********

Daga ranar 8 zuwa ranar 14 ga watan da muke ciki, ana ci gaba da mika wutar wasannin Olimpic a jihar Mongoliya ta gida mai ikon aiwatar da harkokinta na kanta da lardin Helongjiang da lardin Jilin. A lokacin mika wutar, wuraren da wutar ta ratsa sun nuna himmarsu ga aikin mika wutar ta hanyoyin musamman daban daban nasu. A ranar 12 ga watan da muke ciki, a lokacin da aka mika wutar a birnin Harbin na lardin Helongjiang, shahararrun 'yan wasan raye-raye a kan kankara na kasar Sin malama Shen Xue da Malam Zhao Hongbo sun mika wutar a karo na farko, kuma sun kunna wutar a kwano. Mr Zhao Hongbo ya bayyana cewa,

na yi farin ciki sosai, kuma na burge sosai. A shekarar 1998, na taba shiga bikin bude wasannin Olimpic na yanayin hunturu a kasar Japan, na ga wutar wasannin Olimpic da aka mika kuma ta wuce a inda nake tsayawa, na burge sosai da sosai, ban yi tsammanin cewa, yau a garina ne na shiga aikin mika wutar, kai, ban yi kome ba, sai farin ciki zuwa farin ciki, na burge sosai fiye da kima.

******* ******* *********

A ranar 8 ga watan da muke ciki, an soma aiki da babban ginin musamman na tashi da saukar jiragen saman da ake yin amfani da shi domin wasannin Olimpic.

********* ******** *********

Sabon adadin da hukumar yawon shakatawa ta birnin Beijing ta bayar ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 11 ga watan da muke ciki, yawan masu yawon shakatawa da za a karba a lokacin wasannin Olimpic na Beijing zai kai dubu 120, watakila mutanen da za su zo nan birnin Beijing a lokacin za su karuwa, an kimanta cewa, yawansu zai kai dubu 450.

*** **** **** ****

Masu sa kai ga wasannin Olimpic da yawansu ya kai 40 na jami'ar da ake kira "The University of Newcastle ta kasar Australiya sun sauko nan birnin Beijing, ya zuwa yanzu, dukkan masu sa kai na kasashen ketare da yawansu ya kai 292 sun riga sun sauko nan birnin Beijing.

A ranar 10 ga wannan wata, shugaba mai kula da aikin soja na cibiyar ba da jagoranci ga aikin tsaro na wasannin Olimpic na Beijing Mr Tian Yixiang ya bayyana cewa, an riga an kammala aikin shimfida rundunar sojoji masu tsaron wasannin Olimpic, rundunar sojojin tana da karfin kammala aikin tsaron wasannin Olimpic da gwamnatin kasar Sin ta dora musu nauyin.

***** ***** ********

A ranar 12 ga wannan wata, mataimakin babban sakataren kwamitin wasannin Olimpic na kasar Sin Mr Jiang Zhixue ya karbi ziyarar da manecma labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, tsayayyen matsayin da kasar Sin ta dauka na yaki da maganin kara kuzari da za a yi amfani da shi ba zai canja ba ko kadan tun daga farko har zuwa karshe, idan an gano 'yan wasan kasar Sin da suka keta dokar hana yin amfani da maganin kara kuzari a wasannin Olimpic, to za a hana wannan dan wasan da zai shiga kowace gasar da za a shirya a duk rayuwarsa.

Mr Jiang Zhixue ya bayyana cewa, wajen yaki da maganin kara kuzari da za a yi amfani da shi a gasar wasannin motsa jiki, kasar Sin ba za ta daina aikinta na kin yin amfani da shi ba saboda an kawo karshen wasannin Olimpic. A cikin gwagwarmayar da ake yi don yaki da maganin kara kuzari a nan gaba a dogon lokaci, kasar Sin ita ce jarumar da ke da tsayayyar niyya har abada.(Halima)