Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 15:47:07    
Neman kalaman fatan alheri ga kumbo mai lambar bakwai samfurin "Shenzhou"

cri

A watan Oktoba na shekarar 2008, kasar Sin za ta harba kumbon daukan mutane mai lambar 7 samfurin "Shenzhou" ta hanyar yin amfani da roka F mai lambar 2 samfurin "Changzheng". 'Yan sama-jannati na kasar Sin za su yi kokarin tafiya a cikin sararin sama bisa karo na farko.

Tashar internet ta CRI wato "CRI Online" da kungiyar manazarta taurari ta kasar Sin sun shirya wani aiki tare musamman domin neman kalaman nuna fatan alheri daga wajenku, masu yin amfani da internet a duk fadin duniya, taken aikin shi ne "Zan shiga samarin sama tare da kumbo mai lambar 7 samfurin Shenzhou". Kuna iya aiko mana fatan alheri ta hanyoyi daban daban, alal misali rubuta magana da dauka hoto da rera waka da dauka murya da flash da DV da dai sauransu. Kwamitin shirya aikin zai zabi wasu daga cikinsu domin shigar da su cikin sararin sama tare da kumbon.

Za a gama aikin kafin masalin karfe 8 da safe na ran 8 ga watan Satumba na shekarar 2008, agogon Beijing. Muna fatan za ku rubuta kalaman fatan alheri a kasa kai tsaye ko za ku aiko mana ta adireshinmu na e-mail wato hausa@cri.com.cn

Sai mun ji daga gare ku, kuma muna son fatan alherinku zai samun yaduwa a cikin sararin sama.