Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 15:41:05    
Gasar neman zama zakara a cikin kauyen 'yan wasannin Olympics

cri

Game da 'yan wasa na wurare daban daban na duniya, gasar wasannin Olympics wani wuri ne da ke iya nuna kwarewarsu a fannin gasanni, haka kuma ita wani babban dakali ne da ke iya yin cudanya da kuma samun abokai. A cikin kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing, a kan shirya wata gasar musamman a ko wace rana, wato wasan kwallon kafa a kan tebur domin sakin jiki da kuma kara zumuncin da ke tsakanin 'yan wasa. To yanzu ga cikakken bayani.

Ihu iri daya amma wuri ya sha bamban. A wannan karo, an yi ihu kamar haka ne a cibiyar nishadi ta kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing a maimakon filaye da dakunan wasannin Olympics. Da zarar ka ji wannan, watakila ba ka san abin da aka yi ba, a hakika dai wannan ita ce wata gasa ta musamman da ake yi a kauyen 'yan wasannin Olympics, wato wasan kwallon kafa a kan tebur. Kada ka yi rashin mai da hankali a kan wannan karamin tebur, lalle ya taka muhimmiyar rawa a cikin zaman rayuwar 'yan wasa a kauyen.

Song Wei, shugaban kungiyar tafiyar da wannan harka ya gaya wa wakilinmu cewa, 'yan wasa sun nuna sha'awa sosai ga irin wannan wasa, shi ya sa kauyen 'yan wasannin Olympics ya tsai da kudurin shirya wata gasa dominsu, wato 'yan wasa suna iya yin rajista kan shiga gasar a rana daya kafin yinta, kuma bisa ka'idojin wasannin Olympics, za a samu lambobin zinariya da azurfa da kuma tagulla a ko wace rana. Yaya 'yan wasa ke nuna sha'awarsu ga gasar musamman da aka yi? To yanzu bari mu saurari abubuwan da 'yan wasa suka ji daga zuciyarsu.

"Yana da ban sha'awa sosai, na ji dadin gasar kwarai. Ko da yake muka ci tura, amma a cikin gasarmu, dukkan bangarori biyu suna da karfi sosai. Na fara yin gasar tun yarantakata, shi ya sa ina son zama zakara kwarai da gaske."

Har ma bai bar wurin yin gasar ba, sai nan da nan wannan dan wasan kasar Pakistan mai suna Salman Akbaiz ya fara yin koke-koke kan faduwarsu. Shi da abokinsa na wasa sun ci tura a cikin gasa ta kusan karshe da ke tsakaninsu da wata kungiyar kasar Brazil. Amma ba su son amincewa da faduwarsu ba, kuma sun sake tsayawa a kusa da teburin domin neman gano kwarewar kungiyar 'yan wasa ta Brazil.

Tare da bayani na salon Brazil da aka yi kan wasan kallon kafa, bisa albarkacin lokacin da ya fi jawo hankulan mutane ya yi, an fara karon karshe na gasar a tsakanin kungiyoyi biyu na 'yan wasan kasar Brazil, har ma sun gayyaci sauran 'yan kungiyar kasar don yin bayani kan gasar da kuma daukar hotuna.

A karshe dai, Aurelio Araujo da Cassius Duran sun lashe 'yan uwansu da kuma zama zakara. Sun ji murna kwarai da gaske har ma sun yi tsalle da kuma rungume juna tare da ihu "Mun zama zakara". Ban da wannan kuma Araujo ya gaya wa wakilinmu cewa, wannan lambar zinariya ta musamman tana da ma'ana sosai, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ya samu damar samun dimbin sabbin abokai. Kuma ya kara da cewa,

"Na ji murna sosai kamar na zuba ruwa a kasa na sha, kuma mun shaida cewa, ba kawai kasar Brazil ta nuna gwaninta a wasan kwallon kafa ba, har ma ta yi fintikau a cikin wasan kwallon kafa a kan tebur."(Kande Gao)