A wata mai zuwa, makarantun da ke wurare daban daban na kasar Sin za su shiga wani sabon zangon karatu. Kamar yadda za a yi a sauran wuraren kasar Sin, tun daga ran 1 ga watan Satumba mai zuwa, za a mayar da karatu a makarantun da ke yankunan da girgizar kasa mai tsanani ta galabaitar da su a lardin Sichuan na kasar Sin.
Babbar girgizar kasa mai tsanani da ta afka wa lardin Sichuan na kasar Sin a ran 12 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki ya haifar da manyan hasarori ga lardin Sichuan tare kuma da lardin Shanxi da na Gansu da ke makwabtaka da shi, musamman ma a sakamakon girgizar kasar, dimbin dakunan makarantu sun lalace.
A gun taron manema labarai da aka gudanar a ran 25 ga wata a nan birnin Beijing, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayar da labarin cewa, a cikin lokacin hutu na yanayin zafi na tsawon wata daya da 'yan kwanaki, an share fagen mayar da karatu a makarantu daban daban kamar yadda ya kamata, kuma a ran 1 ga watan Satumba mai zuwa, za a iya mayar da karatu a dukan makarantun da ke yankunan da bala'in ya shafa. Mr.Yang Nianlu, mataimakin shugaban sashen kula da ilmin matakin farko na ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya ce,"Na farko, tare da ma'aikatar gine-gine ne ma'aikatar ilmi ta tsara ma'aunin kimanta dakunan makarantu a yankunan da girgizar kasa ta shafa, wato ke nan aka share fage ga binciken dakunan makarantun a yankunan da girgizar kasa ta shafa kamar yadda ya kamata. Na biyu kuma, mun tura masana da dama a fannin kimanta hasarori sanadiyyar girgizar kasa zuwa yankunan da girgizar kasa ta shafa, don su kimanta yadda dakunan makarantu suka lalace. Na uku, mun yi kokarin gina dakunan makarantu."
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta ware kudin Sin yuan sama da biliyan 2 da miliyan 300 wajen gyara da inganta dakunan makarantun sakandare da na firamare a gundumomi 51 da suka fi fama da girgizar kasa a lardunan Sichuan da Gansu da Shanxi tare kuma da samar musu kayayyakin karatu.
Mr.Xu Wentao, shugaban sashen kula da aikin ba da ilmi na lardin Sichuan, ya ce, "Abu na farko da za mu yi shi ne mu ci gaba da gina dakunan makarantu, kuma bisa cigaban da muka samu a yanzu, muna da imanin mayar da karatu a ran 1 ga watan Satumba mai zuwa."
A sa'i daya kuma, sassan ba da ilmi na kasar Sin suna kokarin daidaita matsalar karancin malamai a yankunan da bala'in ya shafa. A gun taron manema labarai da aka gudanar a ran 25 ga wata, Mr.Song Yonggang, mataimakin shugaban sashen kula da horar da malamai na ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya ce, "Domin daidaita matsalar karancin malamai a yankunan da girgizar kasa ta shafa, shirin guraben aikin malamai na musamman a makarantun kauyuka wanda gwamnati ta gabatar da kudin musamman, wanda kuma ma'aikatar ilmi tare da ma'aikatar kudi da dai sauran sassan da abin ya shafa suka fara aiki da shi a shekarar 2006 zai bai wa makarantun da ke yankuna masu fama da bala'i fifiko. Wato muddin gundumomin da bala'in ya shafa suka gabatar da bukatunsu dangane da guraben musamman, to, za a biya bukatunsu. Gaba daya makarantun da ke yankunan da bala'in ya shafa sun gabatar da guraben musamman 387, kuma ya zuwa yanzu, an riga an tabbatar da malamai 364 a kan guraben, wadanda za su fara aiki a ran 1 ga wata mai zuwa."(Lubabatu)
|