Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 11:56:45    
Kungiyoyin makawa na Afirka sun nuna wasan fasaha a birnin Beijing don maraba da zuwan wasannin Olympics

cri

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kungiyar mawaka ta Kayamba da ta zo daga kasar Kenya ta sa hannu a cikin wasan fasaha mai taken "daren Afirka" wanda yake daya daga cikin jerin wasannin fasaha da ake kiransa "Saduwa a Beijing", da kuma nuna wa 'yan kallo na kasar Sin kide-kiden gargajiya na Afirka a babban dakin taruwar jama'a na Beijing domin bai wa wasannin Olympics fatan alheri, ta yadda Beijing mai dogon tarihi da ke gabashin duniya ya iya fahimtar makekiyar Afirka da kuma himmarta. To yanzu ga cikakken bayani.

Abin da kuke saurara dazun nan murya ce mai dadin ji da 'yan kungiyar Kayamba ta Afirka shida suka yi cikin hadin gwiwa. To, mene ne Kayamba? Game da wannan, Juma Odemba, shugaba kuma mai kula da kide-kide na kungiyar ya gaya mana cewa,

"Kayamba wani kayan kida ne na Afirka. Dalilin da ya sa muka kira kungiyarmu Kayamba shi ne sabo da dimbin kabilu na Afirka su kan rera wakoki bisa harsunansu tare da Kayamba. Kuma mu ma mu kan rera wakoki da harsuna daban daban, muna fatan za mu iya samu wani abu iri daya da ke cikin wakokin, kuma mun samu kayan kida na Kayamba, shi ya sa muke kiranmu 'kungiyar Kayamba'."

An kafa kungiyar mawaka ta Kayamba ta Afirka a shekara ta 1998, wadda ba kawai ta kiyaye halayen musamman na gargajiya na Afirka ba, har ma ta hada su tare da wasan fasaha na zamani na salon POP domin duniya ta sake fahimtar kide-kiden Afirka ta hanyoyin nuna wasan fasaha bisa hanyar zamani da kuma tsara wakoki bisa salon POP. Dukkan membobi 6 na kungiyar mawaka ta Kayamba sun nuna sha'awa sosai ga al'adun kasar Sin, kuma wannan shi ne wata kyakkyawar dama gare su wajen sa kaimi ga wasannin Olympics na Beijing bisa gayyatar da aka yi musu a lokacin cikon shekaru goma da kafuwar kungiyar. Mr. Odemba ya bayyana cewa,

"Wannan na daya daga cikin zarafofi mafi kyau gare mu. Da farko, ba mu taba nuna wake-wakenmu a cikin wasan fasaha da ke da babban matsayi kamar haka ba, kuma mun iya zuwa kasar da ke shirya wasannin Olympics a wannan ranar musamman a madadin kasar mu. Haka kuma abu mafi muhimmanci shi ne muna iya rera wakoki don 'yan kallo da ba su taba saurarar wakokinmu a da ba, gaskiya ne sun ji dadin kide-kidenmu kwarai, lalle wannan wani abu ne da ke da matukar kyau."

Domin dace da dabi'ar 'yan kallo Sinawa, kungiyar mawaka ta Kayamba ta zabi wata wakar kasar Sin da dukkan Sinawa ke sani sosai, wato "Zuciyata ta kishin kasar Sin".

Mr. Odemba ya gaya mana cewa,

"Muna son fahimtar sauran al'adu, shi ya sa lokacin da muke cikin shirin nuna wasan fasaha a wani wuri, mu kan yin iyakacin kokarinmu wajen samun abubuwan da 'yan kallo na wurin ke fahimta sosai. Mun zabi wasu wakoki, amma a karshe dai mun zabi wannan waka mai taken 'Zuciya ta ta kishin kasar Sin', dalilin da ya sa haka shi ne sabo da tana da ma'ana sosai, wato kishin kasa da ta bayyana musamman a lokacin wasannin Olympics. Ko shakka babu mun sha wahala sosai wajen koyonta, amma mun ji alfahari yayin da muke rera wakar, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da muke iya zuwan kasar Sin da kuma jin dadi tare da 'yan kallo Sinawa tare."(Kande Gao)