Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 16:11:47    
Kasar Somaliya ta yi alfahari da shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
Bayan da aka kammala zagaye na farko na kwarya-kwaryar gasar gudu ta mita dari 2 ta mata da aka yi a ran 19 ga wata a filin wasannini motsa jiki na kasar Sin, wato ""Shekar Tsuntsu", lokacin da ake taya murna ga wadanda suka samu nasarar shiga zagaye mai zuwa, mai yiyuwa ne ba wanda ya sa ido kan wata 'yar wasa wadda ta yi shiru ta nufi gefen filin wasannin motsa jiki ba.

Wannan 'yar wasa ita ce Samiya Yusuf Omar wadda ba ta kai shekaru 18 da haihuwa ba ta zo daga kasar Somaliya, wato kasa ce da ke kuriyar Afirka. A gun wannan zagaye na farko na kwarya-kwaryar gasar gudu ta mita dari 2 ta mata, tana karshe daga cikin dukkan 'yan wasa mata. Sakamakon haka, ba ta samu izinin shiga zagaye na biyu ba.

Amma, a matsayin wata 'yar wasa kadai da ta zo daga kasar Somaliya inda aka yi yaki har na tsawon shekaru 17, ya kamata a girmama ta sabo da ta shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing a madadin kasarsu. Kuma an yi alfahari sosai da ganin kwazo da himma da kokarin da ita da wani dan wasan kasar Somaliya daban, wato Abdinasser Said suka yi a gun gasanni.

Ba ma kawai gasar wasannin Olympic ta Beijing ta mika wa jama'ar kasar Somaliya labarun zaman lafiya ba, har ma ta kawo su abubuwa masu ban sha'awa. Lokacin da 'yan kallo na Somaliya suka ga 'yan uwansu suke gasa da 'yan wasa na sauran kasashen duniya tare a filayen wasannin motsa jiki na Olympic, jama'ar Somaliya wadanda suke shan wahalhalun yake-yake sosai sun ji suna kusantar da sauran yankunan duniya da zaman lafiya.

"Wasannin motsa jiki za su iya hada kan jama'a, ina fatan wadannan 'yan wasan kasar Somaliya za su zama alamar yin hadin guiwa a tsakanin jama'ar Somaliya", a cewar Abdunasser Gureid, wakilin gidan rediyon Sheikhbelli na Mogadishu.

Ko da yake yawancin mazauna birnin Mogadishu ba su da karfin biyan kudin sayen akwatunan talabijin da sauran na'urorin talabijin, amma a ran 8 ga wata, mutane da yawa sun je gidajen abokai da na danginsu domin kallon bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma sun jira fitowar 'yan wasan kasarsu a gun wannan gaggarumin bikin wasannin motsa jiki.

"Lokacin da na ga an daga tutar kasar Somaliya a gun bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing, jikina ya yi girgiza cike da annashuwa", a cewar Hassan Gurei, wani mazauni Mogadishu.

A cikin shekara daya da ta gabata, an samu hare-hare iri iri kusan a kowace rana a birnin Mogadishu. Fararen hula sun fi samun hasara a cikin wadannan hare-hare. Wasu mutane sun yi tsammani cewa, yanzu mutane da yawa suna fuskantar matsalolin karancin abinci da kasancewarsu a nan duniya a kowace rana, ba abin da ya wajaba ba ne a bata lokaci domin kallon shirye-shirye masu ban sha'awa kamar su gasannin wasannin Olympic.

Amma Yusuf Osman, mazauni birnin Mogadishu wanda yake sha'awar wasannin motsa jiki yana ganin cewa, wasannin Olympic ba shirye-shirye masu ban sha'awa kawai ba, su wata dama ce da ke hada kan kasashe daban daban da kabilu daban daban. Ya ce, "Za mu iya koyon abubuwa da yawa daga wasannin motsa jiki na Olympic, irin wadannan abubuwa za su iya taka rawa wajen daidaita matsalolin da kasar Somaliya ke fuskanta yanzu. Wasannin motsa jiki na Olympic sun bayyana cewa, ko da yake ya kasance da ra'ayoyi daban daban a tsakanin dan Adam, sun iya tafiya wuri daya ta hanyar zaman lafiya domin yin gasa cikin lumana. Ina tsammani, wannan ma'ana ce ta wasannin motsa jiki na Olympic."

Lokacin da Dahapo Ali Igar, wato mahaifiyar Samiya take ganawa da wakilinmu, tana alfahari sosai domin diyyarta ta samu damar shiga gasar wasannin Olympic a yayin da take karami haka.

Amma abin bakin ciki shi ne Mohammad Ado, mai horaswa na Samiya bai raka ta zuwa Beijing ba sakamakon karancin kudaden wasannin motsa jiki. Malam Ado yana da imani cewa, "Samiya za ta iya samun wata lambar yabo domin kasar Somaliya a wata rana nan gaba."   (Sanusi Chen)