Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 15:13:23    
Mr. Qin Huabei, mai yin kukumar Tianqin ta kabilar Zhuang ta kasar Sin

cri

A gundumar Longzhou ta birnin Chongzuo na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin, da akwai wata fasahar kabila mai dogon tarihi wato fasahar kukuma mai sunan Tianqing, Mr. Qin Huabei mai shekaru 43 da haihuwa kuma mai yin kukumar Tianqin ya yi matukar kokari domin yayata da kuma kyautata fasahar Tianqin kusan duk zaman rayuwarsa. To, jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani game da dan kabilar Zhuang mai sunan Qin Huabei da fasaharsa ta kukumar Tianqin.

Jama'a, wakar da kuka saurara dazu wata wakar gargajiya ce da Mr. Qin Huabei da diyarsa suka rera tare ta hanyar kukumar Tianqin. Kukumar Tianqin wata irin kukuma ce wadda take da tarihi na shekaru fiye da 1,000, akan yi amfani da irin wannan kayan kida ne a wuraren da mutane 'yan kabilar Zhuang suke zama a kasar Sin.

Mr. Qin Huabei, dan kabilar Zhuang wanda aka haife shi a gundumar Longzhou ta birnin Chongzuo na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta, kakansa wani dan fasahar goga kukumar Tianqin ne, sabo da haka tun yarantakarsa, Mr. Qin Huabei ya fara kaunar irin wannan kukuma, ya ce,

"Tun lokacin da na ke yaro, na fara koyon fasahar yin kukumar Tianqin, a duk lokutan da kakana yake yin kukumar, na kan zauna a gefensa don yin kollo a sace, kakana ba ma kawai ya iya yin kukuma ba, kuma ya iya goga kukumar da kyau, kidan kukumar da ya yi yana da dajin ji, sabo da haka ni ma ina son wannan fasaha."

Cikin shekaru na 80 na karnin da ya wuce, Mr. Qin Huabei ya shiga cikin kungiyar 'yan fasaha na wurin da yake zama, kuma ya fara kyautata fasahar yin kukumar Tianqin, amma sabo da a lokacin ba a mai da muhimmanci sosai wajen kiyaye irin wannan fasaha mai dogon tarihi ba, shi ya sa kusa an sami rishin ci gaba da kiki-kaka wajen wannan aiki.

Bayan da aka shiga cikin karni na 21, domin kubutar da fasahar yin kukumar Tianqin wadda take kusan karewa, gwamnatin jihar ta rubanya kokari domin kiyaye da kuma bunkasa al'adun kukumar Tianqin, kuma ta kafa wata kungiya masu goga kukuma ta mata wadda take hade da 'yan mata 15 na gundumar Longzhou wadanda matsakaicin yawan shekarunsu ya kai 21 da haihuwa, wadanda kuma a shirye suke su goga kukumar Tianqin a gun bikin fasahar da za a shirya a wancan shekara a birnin Nanning. Gwamnatin gundumar kuma ta gayyaci Mr. Qin Huabei da zai yi kukumar Tianqin domin wadannan 'yan mata. Da ya ji wannan labari ya yi farin ciki sosai ya ce,

"A wancan lokaci shugaban hukumar al'adu da wasan motsa jiki ya gaya mini wannan lamari, daga baya na yi aikin da ya danka mini, kuma na kware wajen yin kukumar Tianqin domin na taba yin wannan aiki lokacin da nake cikin kungiyar 'yan fasaha, amma ban taba yin su a fili ba."

Sabo da haka, Mr. Qin Huabei ya kebe wani daki na gidansa musamman domin yin kukumar Tianqin, kuma ya yi aikin ba dare ba rana. A gun bikin rera wakokin gargajiya na kasashen duniya na 5 da aka yi a watan Nuwamba na shekarar 2003 a birnin Nanning, wadannan 'yan mata na gundumar Longzhou sun dauki kukumar Tianqin da Mr. Qin Huabei ya yi da hannunsa, wasan da suka nuna ya jawo sha'awar dukkan 'yan kallo da ke wurin kwarai da gaske.

Daga shekarar 2003, "Kungiyar 'yan mata masu goga kukumar Tianqin" ta taba nuna wasanni sau da yawa a kasashen waje ciki har da Austria da Jamus, kuma an sayar da kukumar Tianqin da yawansu ya wuce 1,300 da Mr. Qin Huabei ya kera a kasashen ketare ciki har da Amurka da Japan.

A watan Yuni na shekarar 2007 a babban dakin taruwar jama'a da ke nan birnin Beijing, an yi babban taro na farko na nada sunayen mutane masu nuna fiffiko wajen gadar al'adun gargajiya na kasar Sin, bisa matsayinsa na gwani mai yin kukumar Tianqin daya kawai na kasar Sin ta yanzu, Mr. Qin Huabei ya sami sunan mai nuna fiffiko wajen gadar al'adun gargajiya na kasar Sin tare da sauran mutane 166 da suka zo daga kabilu daban-daban na kasar.