Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 15:12:06    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Jiya malaman koyarwa da dalibai 38 na kolejin masana'antu da kasuwancin jihar Ningxia sun zo nan birnin Beijing domin samun horo, sabo da a lokacin wasannin Olimpic da na wasannin Olimpic na nakasassu za su samar da hidima wajen dafa abinci domin baki musulmi fiye da 6,000 na kasar Sin da na kasashen waje da ke cikin kauyen wasannin Olimpic.

A ran 18 ga watan Janairu na wannan shekara, bisa alhakin da kwamitin shirya wasannin Olimpic ya danka masa, hadaddiyar kungiyar dafa abinci ta kasar Sin ta yi jarrabawa ga dalibai 60 na kolejin masana'antu da kasuwancin jihar Ningxia ta hanyar baka da kuma rubutu, kuma ta zabi dalibai 50 daga cikin su. Daga baya kuma an zabi na mataki na 2 daga wajen halayyan mutane da kuma siyasa, a karshe an zabi dalibai 36 da malaman koyarwa guda 2, daga cikin su kuma da akwai mata 2, dukkansu sun samu horo daga ran 19 ga watan Mayu zuwa tsakiyar watan Yuli a kolejinsu daga fannin koyon Turanci da ingancin abinci da nuna kyakkyawan halayen da'a cikin sana'a.

An ce, kungiyar masu yin hidima wajen dafa abinci domin

wasannin Olimpic ta wannan koleji kungiya ce daya kawai da

Ke wakiltar jihar Ningxia domin yin hidima ga wasannin Olimpic wajen dafa abinci.

---- Kwanan baya a nan birnin Beijing, Mr. Kurexi Maihesuti, mataimakin shugaban jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya bayyana cewa, jihar Xinjiang tana da imani wajen yaki da ta'addanci, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta dauki mataki fiye da kima ba kan matsalar yaki da ta'addanci.

A gun taron manema labarun da aka shirya a wannan rana a cibiyar watsa labaru ta kasa da kasa ta shekarar 2008 da ke nan birnin Beijing, Mr. Maihesuti ya ce, duk wani danyen aikin da aka yi domin tauye manufar dinkuwar kasar Sin daya, da jawo baraka ga jihar Xinjiang, za a murkushe su. 'Yan ta'adda ba su da babban karfin kamar yadda wasu kafofin watsa labaru suka yi farfaganda ba, a hakika kuwa yawancinsu tumaki ne ba tare da mai kiwo ba. Ya kuma bayyana cewa, duk wata kasar da ta shirya wasannin Olimpic dukkansu suna son samun tabbaci ga yin wasannin cikin kwanciyar hankali sosai, sabo da haka ayyukan tsaron da kasar Sin ke yi ba abun mamaki ba ne ko kadan, kuma ba su wuce yadda ya kamata ba. Gwamnatin jihar Xinjiang da ta kasar Sin dukkansu sun yi ayyuka da yawa domin tsaron wasannin Olimpic, sabo da haka za a iya zuwan nan kasar Sin don halartar wasannin Olimpic cikin kwanciyar hankali.(Umaru)