Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 15:07:18    
Wata hirar da aka yi a tsakanin wakilinmu da Mr. Alex Gilady, wani memban kwamitin wasannin motsa jiki na Olympic na kasa da kasa

cri

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu a nan Beijing, da farko dai, Mr. Alex Gilady ya yaba wa kokarin da kasar Sin ta yi wajen kyautata muhalli. Yana fatan za a iya fahimta cewa, duniyarmu tana da hanyoyin da ta saba bi na halitta. Bai kamata a kyale kokarin da kasar Sin ta yi wajen cika alkawarin kyautata muhalli ba sabo da yanayi maras kyau na wasu lokuta. Mr. Alex Gilady ya ce, "Kasar Sin ta yi namijin kokari sosai wajen kyautata muhalli. Yau da shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta soma zuba kudade da yawa wajen kyautata muhalli, alal misali, ta dauki matakai na dasa bishiyoyi da itatuwa da ciyayi da rage yawan iskar da motoci ke fitarwa da rage yawan kayayyaki masu gurbata muhalli da masana'antu ke fitarwa, har ma ta dakatar da aikin gine-gine da sauran matakai domin kyautata muhalli. Amma duniyarmu tana tafiya bisa ka'idojin da ta saba bi na halitta. Mai masaukin gasar yana fatan matakan da ya dauka za su iya lashe irin wadannan ka'idojin halitta."

Mr. Alex Gilady, mai shekaru 66 da haihuwa shi ne memban kwamitin Olympic na kasa da kasa na farko da ya zo daga kasar Isra'ila. Ya riga ya halarci gasannin Olympic har sau 9 a mukami daban daban. A ganin Mr. Gilady, birnin Beijing ya riga ya cika alkwarin da ya dauka lokacin da yake neman izinin shirya wata gasar Olympic, wato ya dauki alkawarin cewa zai shirya wata gasar Olympic ba tare da gurbata muhalli ba. Mr. Gilady ya ce, "Haka ne, babu kuskure ko kadan. Ban taba ganin wani birni mai kyaun gani kamar haka ba. Ana ganin ciyayi da furannin da aka sanya su a cikin faranti miliyan 40. Wadannan matakai suna aiki kamar yadda ya kamata. Ya kamata birnin Beijing ya yi alfahari domin yana gudanar da gasar Olympic cikin yanayi mai tsabta."

Mr. Gilady ya kara da cewa, abubuwan da ya kamata birnin Beijing ya yi alfahari suna da yawa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, an yi amfani da dimbin fasahohin kiyaye muhalli da na tsimin makamashi lokacin da ake gina sabbin dakuna da filayen motsa jiki na gasar Olympic. An kuma kawatar da su sosai. Alal misali lokacin da ake gina cibiyar ninkaya ta kasar Sin, wato a kan kira ta "Water Cubic", an yi amfani da wata fasahar yin tsimin makamashi, wato za a iya yin amfani da hasken rana wajen daidaita haske da zafi a cikin wannan cibiyar ninkaya. Sabo da haka, za a iya yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli. Mr. Gilady ya yaba wa wannan fasaha sosai, ya ce, "Na taba shiga wannan cibiyar ninkaya, wato Water Cubic. Ba a iya samun abin kuskure ba. An yi amfani da wadannan zane-zane ne ba domin kyaun gani kawai ba, har ma yana amfana wa gasar. Yanzu kome yana nan kamar yadda ya kamata. Muna fatan 'yan wasa za su samu sakamako mai kyau a wannan cibiyar."

Shirya wata gasar Olympic ba ma kawai abin alfahari ne na Sinawa ba, har ma wani gagarumin biki ne da ke jawo hankulan duk duniya. Mr. Gilady ya ce, yanzu za a iya ganin abubuwan da suke da nasaba da gasar Olympic a ko'ina a kasar Sin. An riga an shigar da ruhun Olympic a duk fadin kasar Sin. Gasar Olympic ta Beijing za ta zama dukiya mai daraja ga kasar Sin. Mr. Gilady ya ce, "Gasar Olympic ta Beijing za ta sama wa kasar Sin dukiyoyi masu daraja, alal misali wasu muhimman ayyukan na yau da kullam, kamar su tagwayen hanyoyin mota da hanyoyin jiragen kasa da dai makamantansu tare da dakuna da filayen motsa jiki masu kyaun gani. Kuma Sinawa za su yi alfahari sosai sabo da sun taba bayar da gudummowarsu wajen shirya wata kasaitacciyar gasar Olympic, kuma za su halarci gasar Olympic da kansu." (Sanusi Chen)