Zou Shiming
Yau ranar 24 ga wata, an shiga kwana na 16 wato kwana na karshe na gasar wasannin Olympics ta Beijing, an fitar da lambobin zinariya 12.
A gasar gudun Marathon ta maza, 'dan wasa na kasar Kenya Wansiru Samuel Kamau ya samu lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajimtar Olympics.
A gasar lankwashe jiki na nuna fasahohin na duk fannonin da ke tsakanin kungiya da kungiya, kungiyar kasar Rasha ta samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo 48, shahararren 'dan wasa na kasar Sin Zou Shiming ya samu lambar zinariya.
A gasar kwallon raga ta maza, kungiyar Amurka ta samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo 54, 'dan wasa na kasar Mongolia Badar-Uugan Enkhbat ya samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo 60, 'dan wasa na kasar Rasha Tishchenko Alexey ya samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo 69, 'dan wasa na kasar Khazakstan Sarsekbayev Bakhyt ya samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo 81, 'dan wasa na kasar Sin Zhang Xiaoping ya samu lambar zinariya.
A gasar karshe ta kwallon kwando ta maza, kungiyar kasar Amurka ta samu lambar zinariya.
A gasar dambe ta maza ta ajin kilo fiye da 91, 'dan wasa na kasar Italiya Roberto Cammarelle ya samu lambar zinariya.
A gasar kwallon ruwa ta maza, kungiyar kasar Hungary ta samu lambar zinariya.
A gasar kwallon hannu ta maza, kungiyar kasar Faransa ta samu lambar zinariya.(Danladi)
|