Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-23 22:04:42    
Labarai na gasanni na kwana ta 15

cri

Yau ranar 23 ga wata ne aka shiga kwana na 15 da soma gasar wasannin Olympics, za a fitar da lambobin zinariya 32 a wannan rana. Ya zuwa karfe 9 na dare  bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 22.

A cikin gasar tseren keke ta kewaye gari ta mata, 'yar wasa ta kasar Jamus Spitz Sabine ta samu lambar zinariya. 'dan wasan kasar Faransa Absalon Julien ya samu lambar zinariya a cikin gasar tseren keke ta kewaye gari ta maza.

An fitar da lambobin zinariya 6 na karshe a cikin gasannin tseren kwale-kwale. A cikin gasar tseren kwale-kwale ta mita 500 ta tsakanin mace da mace, 'yar wasa ta kasar Ukraine Osypenko-Radomska Inna ta samu lambar zinariya. A cikin gasar tesren kwale-kwale ta mita 500 ta tsakanin maza biyu biyu, 'yan wasan kasar Sin Meng Guanliang da Yang Wenjun sun samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, kungiyar 'yan wasan kasar Rasha ta samu lambar zinariya a cikin gasar salon-iyo ta tsakanin kungiya kungiya. Kungiyar 'yan wasan kasar Sin ta samu lambar tagulla, wannan ya zama sakamako mafi kyau gare ta a tarihi.