Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-22 22:20:46    
Labarai na gasanni na kwana ta 14

cri

An shiga kwana na 14 na soma gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma ana cigaba da gasa domin samun lambar zinariya, ran nan za a fitar da adadin lambobin zinariya 21.

A cikin gasar tseren keke mai kananan tayoyi ta mata, Chausson Anne-Caroline, 'yar wasan kasar Faransa ta sami lambar zinariya.Wannan shi ne karo na farko da aka shigo da gasar tseren keke mai kananan tayoyi cikin gasar wasannin Olympic, shi ya sa lambar zinariya da 'yar wasan Faransa ta samu ta kasance lambar ziyariya ta farko ta gasar tseren keke mai kananan tayoyi a cikin tarihin wasannin Olympic.

A cikin gasar tseren keke mai kananan tayoyi ta maza, Maris Strombergs, dan wasan kasar Latvia ya sami lambar zinariya, wato lambar zinariya ta farko ta gasar tseren keke mai kananan tayoyi ta maza a cikin gasar wasannin Olympic.

A cikin karshen gasar kwallon raga ta rairayin bakin teku ta maza ta wasannin Olympic, Todd Rogers da Phil Dalhausser, 'yan wasan kasar Amurka da ke matsayi na farko a cikin duk duniya sun lashe 'yan wasan kasar Brazil da ci 2 da 1, sun sami lambar zinariya. 'Yan wasan kasar Amurka sun sami lambar zinariya ta maza da ta mata a cikin gasar kwallon raga ta rairayin bakin teku.

A cikin gasar iya tafiya da sauri ta maza ta tsawon kilomita 50 da aka yi a wasannin Olympic na Beijing, Alex Schwazer, dan wasan Italy da shekarunsa ya kai 24 da haihuwa, ya sami lambar zinariya, kuma ya karya natsayin bajinta da dan wasan kasar Rasha ya yi a cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata a cikin gasar wasannin Olympic.

A cikin gasar tseren kwale-kwale ta mita 1000 tsakanin maza biyu biyu, kungiyar 'yan wasan kasar Jamus ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar tseren kwale-kwale ta mita 1000 tsakanin maza hudu hudu, kungiyar 'yan wasan kasar Belorussia ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar gudu ta mita dubu 5 ta mata, 'yar wasa ta kasar Habasha Tirunesh Dibaba ta samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, a cikin gasar dogon tsalle ta mata, 'yar wasa ta kasar Nijeriya Okagbare Blessing ta samu lambar tagulla. 'Yar wasa ta kasar Brazil Maggi Higa ta samu lambar zinariya.

Kuma a cikin gasar gudu ta ba da sanda tsakanin mata hudu na mita 4, kungiyar 'yan wasan kasar Nijeriya ta samu lambar tagulla. Kungiyar kasar Rasha ta samu lambar zinariya.