Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-22 19:12:01    
Bangaren 'yan sanda na Sin na da aniyar bada kyakkyawan tsaro ga gudanar da gasa wasannin Olympics tare da nasara

cri

Ko kuna sane da cewa, an gudanar da zama na 12 na majalisar hukumar kula da harkokin yaki da ta'addanci tsakanin shiyya-shiyya ta kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO a ran 3 ga watan da muke ciki a nan birnin Beijing, inda kasashe daban-daban mahalartan taron suka tattauna wannan batun musamman kan aikin tsaron gasar wasannin Olympics ta Beijing da kuma hadin kai da ake yi wajen yaki da ta'addanci. A gun taron, mataimakin ministan tsaron zaman lafiyar jama'a na kasar Sin Mr. Meng Hongwei ya fayyace cewa, babbar barazana da gasar wasannin Olympics ta Beijing take fuskanta ta zo ne daga kungiyar 'yan ta'addanci ta Gabashin Turkstan . Amma, gwamnatin kasar Sin da sassan tsaron zaman lafiyar jama'a na kasar sun rigaya sun dauki jerin tsauraran matakai. Lallai kasar Sin na da aniyar bada tabbaci ga samun kyakkyawan tsaro don gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara.

An labarta cewa, a wannan rana, daraktan kwamitin hukumar kula da harkokin yaki da ta'addanci tsakanin shiyya-shiyya ta kungiyar SCO da kuma jami'an da abin ya shafa sun taru gu daya, inda bangaren kasar Sin ya bayyana wa sauran bangarori halin share fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing; Sa'annan bangarori daban-daban gaba dayansu sun yi nazari kan matakan da za a dauka don yin hadin gwiwa a fannin tsaron gasar wasannin Olympics; Bugu da kari, kowanensu ya bada rahoto kan bayanan asiri da yake rike da su a game da yiwuwar barazanar da 'yan ta'adda za su yi wa gasar wasannin Olympics. A lokacin da yake karbar ziyarar da manema labaru suka yi masa, Mr. Meng Hongwei ya fadi cewa, kasar Sin na sa ran alheri ga yanayin tsaron gasar wasannin Olympics. A lokaci guda, tana matukar kokarin riga-kafin barazana da mai yiwuwa ne za a gamu da ita daga muhimman fannoni uku. Yana mai cewa:" Fanni na farko shi ne, kungiyoyin kasa da kasa na ta'addanci da kuma 'yan ta'adda za su iya yin amfani da wannan dama don kai harin ta'addanci ga wassu kasashe da mutane da kuma gine-gine na musamman. Fanni na biyu, game da kasar Sin dai, babbar barazanar ta'addanci ta zo ne daga kungiyar ta'addanci ta Gabashin Turkstan. Kwanan baya ba da dadewa ba, wannan kungiya ta yi shela a filli kan internet a dukkan fadin duniya cewa za ta dauki matakin kai hari ga gasar wasannin Olympics ta kasar Sin. Fannin na uku wato na karshe, shi ne ya kasance da yiwuwar aikata wassu manyan laifuffukia, wadanda ka iya kawo barazana ga kwanicyar hankali".

Bisa wannan hali dai, gwamnatin kasar Sin da sassan tsaron zaman lafyar jama'a na kasar sun kafa wata hukuma kakkarfa ta musamman dake kunshe da sojoji da kuma 'yan sanda. A lokaci guda, an kuma gudanar da ayyukan riga-kafi a fannin tsaro a wurare daban-daban na duk kasa daga dukkan fannoni. Kazalika, an kaddamar da jerin shirye-shiryen ko-ta-kwana don tinkarar harin ta'addanci.

Jama'a masu sauaro, ko kuna sane da cewa, ma'anar sunan Gabashin Turkstan ita ce wassu kungiyoyin ta'addanci a ciki da wajen jihar Sinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wadanda kuma suke yin amfani da dabarar kai harin ta'addanci cikin hakilin banza na kafa " Kasar Gabashin Turkistan".

Mr. Meng Hongwei ya ci gaba da cewa, da yake aka kara yin bincike da kuma samun bayanan asiri, shi ya sa gwamnatin kasar Sin ta riga ta dakile harkokin ta'addanci da wassu kungiyoyin ta'addanci na " Gabashin Turkistan" suka tayar kafin a gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Yana mai cewa: " Mun dauki jerin tsauraran matakai a fannin samun bayanai asiri da kuma yin bincike. Saboda haka ne, muka dakushe wasssu kungiyoyin Gabashin Turkistan.

Ban da wadannan kuma gwamnatin kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da sauran kasashe a fannin tsaron gabas wasannin Olympics ta Beijing da kuma yaki da ta'addanci. Tuni a watan Satumba na shekarar bara, a nan Beijing, wakilan kungiyar TERPOL, da kungiyar SCO da kuma na sauran kasashe da yankuna 32 sun bayar da wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan tsaron gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A gun taron, wakili Nazarov daga kasar Tajikstan uwar taron ya furta cewa, kasashen kungiyar SCO a shirye suke wajen bada taimakon da ya wajaba ga kasar Sin a fannin tsaron gasar wasannin Olympics ta Beijing. Mr. Nazarov ya furta cewa: " Shugabannin tawagoyin dukkan bangarori sun dauka cewa, wannan muhimmiyar harkar duniya mai ma'anar tarihi wato gasar wasannin Olympics ta Beijing ba ma kawai tana da muhimmmancin gaske ga jama'ar kasar Sin ba, har ma ga jama'ar kasashen Asiya".

Aminai 'yan Afrika, a yanzu haka dai, an shiga matakin karshe na share fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing. Mr. Meng Hongwei ya karfafa cewa: " Kasar Sin na da aniyar ba da tabbaci ga samun kyakkyawan tsaron wannan gagarumar gasa. Yanzu, kasar Sin zaune take da gindinta sosai a fannoni daban-daban. Hakan ya zamo tushe mai inganci ga gudanar da wannan gasa mai kayatarwa cikin nasara". ( Sani Wang )