Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-22 19:01:54    
Muna matukar farin ciki a nan Beijing in ji jagoran tawagar Ghinea- Bissau

cri

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka san cewa, kasar Ghinea-Bissau tana yammacin Nahiyar Afrika. Ko da yake an tafi an bar wannan kasa baya wajen samun gine-ginen wasan motsa jiki, amma duk da haka, jama'ar kasar suna sha'awar wasannin motsa jiki. A wannan gami dai, Ghinea-Bissau ta turo 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle biyu da kuma wani dan wasan kokawa. Jagoran tawagar kasar, Mista Deladier Vieira ya fada wa wakilinmu cewa: " A gun wasannin Olympics, abu mafi muhimmanci a gare mu, shi ne halartar wasannin ba wai samun lambar yabo kawai ba. Muna da 'yan wasa guda uku. Daya daga cikinsu ya riga ya kammala gasar, inda ya yi fice sosai yayin da yake gwada wa duk duniya kyakkyawa fuskar kasar ta Ghinea-Bissau".

A matsayin jagoran tawagar kasar Ghinea-Bissau, Mista Vieira ya taba halartar wasannin Olympics na Sydney da na Aden. A yayin da yake tabo magana kan yadda yake ji a zuciyarsa game da kauyen 'yan wasan Olympics, ya furta cewa :" Dukkan mutane dake zaune a nan suna farin ciki matuka. Na taba halartar wassu gasannin Olympics. A ganina, bai kamata a kira wannan wuri kauyen wasannin Olympics ba, ya kamata a kira shi birnin wasannin Olympics".

Sa'annan Mista Vieira ya buga babban take ga filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing, inda ya fadi cewa: "Lallai ba mu taba ganin irin wadannan gine-gine na zamani ba a da. Ko shakka babu, wadannan filaye da dakunan wasannin sun aza tushe mai inganci ga gudanar da gasanni iri daban-daban masu ban sha'awa lami-lafiya. Daga nan ne muke tabbatar da cewa, kasar Sin na da karfin da take da shi na gudanar da irin wannan gagarumar gasa".

Baya ga wadannan gine-ginen wasannin motsa jiki, zafin nama da jama'ar kasar Sin suka nuna shi ma ya ba shi zurfaffiyar alama a cikin zuciyar Mista Vieira, wanda ya furta cewa: " A nan ne na samu aminai da yawa, musamman ma masu aikin sa kai guda uku na kasar Sin. Mun rinka musaya kyaututtuka da juna. Kuma mun kasance tamkar 'yan babban iyali ne bai daya domin har kullum muna yawon bude ido kan tituna, muna cin abinci tare yayin da muke yin hira cikin halin arziki kan halin kasar mahaifa ta kowane". Mista Vieira ya kara da cewa: " Kusan wata daya ke nan nake yin zama a nan Beijing. Lallai na ji dadi ainun. Na rigaya na saba da komai da komai a nan birnin Beijing."

A lokacin da ake kusan kawo karshen gasar wasannin Olympics ta Beijing, Mista Vieira ya bayyana kyakkyawan fatansa na kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Guinea-Bissau da Sin a fannin wasan motsa jiki, ta yadda kasarsa za ta cimma tudun dafawa wajen bunkasa ayyukan wasannin motsa jiki. Ya mai cewa: " An yi nasarar share fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing. Hakan ya bada wani kyakkyawan misalin koyo ga duk biranen da za su gudanar da gasar wasannin Olympics a nan gaba. Da sahihiyar zuciya ne nake taya kasar Sin murnar samun irin wannan nasara. Kuma ina fatan kasar Sin za ta bada karin taimako ga kasar Ghinea-Bissau wajen bunkasa babban sha'anin wasannin motsa jiki". ( Sani Wang )