Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 21:43:24    
Labarai na gasanni na kwana ta 13

cri

Yau ranar 21 ga wata, an shiga kwana na 13 da soma gasar wasannin Olympics, za a fitar da lambobin zinariya 21 a wannan rana. Ya zuwa karfe 9 na dare bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 12.

A gasar sassarfa ta kilomita 20 ta mata da aka shirya a ran nan da safe, 'yar wasa ta kasar Rasha Kaniskina Olga ta samu lambar zinariya.

A gasar iyo ta Marathon ta kilomita 10 ta maza, 'dan wasa na kasar Holand Van Der Weijden Maarten ya samu lambar zinariya.

A gasar karshe ta kwallon raga a filin rairayi ta mata biyu biyu, 'yan wasa na kasar Amurka wato Walsh Kerri da May-Treanor Misty sun samu lambar zinariya.

A cikin karon karshe na wasan gudu na mita 200, shahararriyar 'yar wasan kasar Jamaica Campbell Brown Veronica, wadda ta zama zakara a cikin wasan a gasar wasannin Olympics da ta gabata ta sake samun lambar zinariya bisa maki dakika 21.74, wanda ya zama maki mafi kyau gare ta

Ban da haka kuma, a gasar kwallon ruwa wato water Polo ta mata da aka yi a wannan rana da dare, kungiyar 'yan wasan kasar Holland ta samu lambar zinariya.

A gasar jefa mash ta mata, 'yar wasa ta kasar Czech Spotakova ta samu lambar zinariya.

A gasar karate ta ajin kilo 57 ta mata, 'yar wasa ta kasar Korea ta kudu Lim Sujeong ta samu lambar zinariya.

Bisa wani labari mai dumi da muka samu, an ce, 'yar wasa ta kasar Sin Chen Ruolin ta samu lambar zinariya cikin gasar tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali mai tsayin mita 10 ta mata.