Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:49:18    
Labarai na gasanni na kwana ta 8

cri

Zhang Ning

Yau ranar 16 ga wata, an shiga kwana na takwas da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing, za a fitar da lambobin zinariya guda 29 a duk ranar, wadda ta zama rana ta farko da ake fi fitar da lambobin zinariya a gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya zuwa karfe 9 na dare bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 22.

A gasar iyon rigingine ta mata ta mita 200, 'yar wasa ta kasar Zimbabuwei Coventry Kirsty ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajimtar duniya.

A gasar iyon da ake kira "Mallam-bude-littafi" ta maza ta mita 100, 'dan wasa na kasar Amurka Phelps Michael ya samu lambar zinariya, wannan ce lamba ta 7 da ya samu a gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A gasar iyo cikin 'yanci ta mata ta mita 800, 'yar wasa na kasar Ingila Adlington Rebecca mai shekaru 19 da haihuwa ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajimta na duniya.

A gasar sassarfa ta maza ta kilomita 20, 'dan wasa na kasar Rasha Borchin Valeriy ya samu lambar zinariya.

A gasar iyo cikin 'yanci ta maza ta mita 50, 'dan wasa na kasar Brazil Cielo Filho Cesar ya samu lambar zinariya.

A gasar harbi da bindiga da sauri ta maza ta mita 25. 'dan wasa na kasar Ukraine Petriv Oleksandr ya samu lambar zinariya.

A gasar kwallon badminton da ke tsakanin mace dai-dai, 'yar wasa ta kasar Sin Zhang Ning ta samu lambar zinariya.

A gasar harbi faifai da bindiga daga fannoni biyu ta maza, 'dan wasa na kasar Amurka Hancock Vincent ya samu lambar zinariya.

A gasar namiji dai dai ta filafilai biyu-biyu ta wasan tseren kwale-kwale, 'dan wasa na kasar Norway Tufte Olaf ya samu lambar zinariya.

A gasar mata biyu-biyu ta filafilin dai dai ta wasan tseren kwale-kwale , kungiyar Romania wato Georgeta Andrunache-Damian, da Viorica Susanu ta samu lambar zinariya.

A gasar mata biyu-biyu ta filafilai biyu-biyu ta wasan tseren kwale-kwale, kungiyar New Zealand wato Evers-Swindell Georgina da Evers-Swindell Caroline ta samu lambar zinariya.

A gasar kokawa cikin 'yanci ta mata ta ajin kilo 48, 'yar wasa ta kasar Canada Huynh Carol ta samu lambar zinariya.

A gasar mace dai dai ta filafilai biyu-biyu ta wasan tseren kwale-kwale, 'yar wasa ta kasar Bulgaria Rumyana Neykova ta samu lambar zinariya.

A gasar maza biyu-biyu ta filafilai biyu-biyu ta wasan tseren kwale-kwale, kungiyar Australiya wato Crawshay David da Brennan Scott sun samu lambar zinariya.

A gasar maza biyu-biyu ta filafili dai dai ta wasan tseren kwale-kwale, 'dan wasa na kasar Australiya Drew Ginn da Duncan Free sun samu lambar zinariya.

A gasar maza hudu-hudu ta filafili dai dai ta wasan tseren kwale-kwale, kungiyar Ingila ta samu lambar zinariya.

A gasar kokawa cikin 'yanci ta mata ta ajin kilo 55, 'yar wasa ta kasar Japan Yoshida Saori ta samu lambar zinariya.

A gasar tseren keken gwajin lokaci ta maza, 'dan wasa na kasar Spain Joan Llaneras ya samu lambar zinariya.

A gasar tseren keke ta hanyar biye da wani ta najimi dai dai, 'dan wasa na kasar Ingila Wiggins Bradley ya samu lambar zinariya.

A gasar takobi maras nauyi kuma gajere da ke tsakanin kungiyoyin mata, kungiyar kasar Rasha ta samu lambar zinariya.

A gasar daukar nauyi ta mata ta ajin koli fiye da 75, 'yar wasa ta kasar Korea ta kudu Jang Miran ta samu lambar zinariya.(Danladi)