Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:54:09    
Labarai na gasanni na kwana ta 12

cri

An shiga kwana na 12 na gasar wasannin Olympics ta Beijing

Yau ran 20 ga wata ne aka shiga kwanan na sha biyu da soma gasar wasannin Olympic. Za a fitar da lambobin zinariya 11. Ya zuwa karfe 9 na dare bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 9.

A cikin gasar iyo na dogon zango wato Marathon ta kilomita 10 ta mata da aka yi a ran nan da safe, 'yar wasan kasar Rasha Larisa Ilchenko ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar kananan kwale-kwale ta mata da aka yi a birnin Qingdao a ran nan, 'yar wasan kasar Sin Yin Jian ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar kananan kwale-kwale ta maza, 'dan wasan kasar New Zealand Tom Ashley ya samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, a cikin gasar salon-iyo ta tsakanin mutane biyu biyu, 'yan wasan kasar Rasha Davydova da Ermakova wadanda suka taba samun lambar zinariya cikin gasar Olympic ta Athens ta 2004 sun sake samu lambar zinariya.

A cikin gasar kokawa cikin 'yanci ta ajin kilo 66 ta maza, 'dan wasan kasar Turkish Ramazan Sahin ya samu lambar zinariya.

A wannan rana da da dare, an yi gasar karate ta ajin kilo 49 ta mata, 'yar wasa ta kasar Sin Wu Jingyu ya lashe wata 'yar wasa ta kasar Thailand ya samu lambar zinariya.