Yau ranar 19 ga wata ne aka shiga rana ta 11 da soma gasar wasannin Olympics, za a fitar da lambobin zinariya 20. Ya zuwa karfe 5 da rabi na yamma bisa agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya 3.
A cikin gasar tseren mutum daya cikin wasanni 3 ta maza da aka yi a wannan rana da safe, 'dan wasan kasar Jamus Frodeno Jan ya samu lambar zinariya.
A cikin gasar tseren kwale-kwale na Laser na mamiji daidai, 'dan kasar Ingila Goodison Paul ya samu lambar zinariya. Kuma 'yar wasa ta kasar Amurka Tunnicliffe Anna ta samu lambar zinaria a cikin gasar tseren kwale-kwale na Laser Radial ta mace daidai.
|