Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:53:29    
Labarai na gasanni na kwana ta 10

cri

Yau ranar 18 ga wata, an shiga kwana na goma na gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 18. Ya zuwa karfe 9 na yamma bisa agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya guda 12.

A cikin gasar tseren mutum daya cikin wasanni 3 mata, 'yar wasa ta kasar Australia Emma Snowsill ta samu lambar zinariya.

A cikin wata gasar tseren kwale-kwale tsakanin maza biyu biyu, kungiyar 'yan wasan kasar Australia ta samu lambar zinariya. Haka kuma kasar Australia ta samu lambar zinariya a cikin wannan gasa ta mata.

A cikin gasar tseren keke ta mata a fili, 'yar wasa ta kasar Holland Marianne Vos ta zama zakara.

Ban da haka kuma, 'dan wasan kasar Sin Chen Yibing ya samu lambar zinariya a cikin gasar rings wato gasar zobe.

A cikin gasar uneven bars na mata, 'yar wasa ta kasar Sin He Kexin ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar tseren keke na bin juna kud da kud na maza a fili ta tsakanin kungiyar maza, kungiyar 'yan wasan kasar Birtaniya ta lashe kungiyar kasar Denmark ta samu lambar zinariya.

Bisa labaru masu dumi dumi da muka samu, an ce, a cikin gasar vaulting horse, 'dan wasan kasar Poland Leszek Blanik ya samu lambar zinariya.

A cikin gasar jefa faifan karfe ta mata, 'yar wasa ta kasar Amurka Trafton ta samu lambar zinariya.

'Dan wasan kasar Belorussia Aramnau ya samu lambar zinariya a cikin gasar daukan nauyi na ajin kilo 105, kuma ya karya bajimtar duniya ta wasan daukan nauyi na sabawa kan wannan aji, da bajimtar duniya ta wannan gasa gaba daya.

Ban da haka kuma, 'yar wasa ta kasar Sin He Wenna ta samu lambar zinariya ta gasar tsalle kan rumfa.

A cikin gasar kwallon tebur ta tsakanin kungiyar maza, kungiyar 'yan wasan kasar Sin ta samu lambar zinariya.