Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:49:22    
Labarai na gasanni na kwana ta 9

cri
Yau, wato ran 17 ga wata, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta riga ta shiga kwana na 9, ya zuwa karfe 9 da kwata na dare,agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 32.

Ban da gasannin da aka yi a rana, a gun gasar wasan Vault ta mata da aka yi a wannan ran da maraice, Hong Un Jong ta kasar Koriya ta arewa ta samu wata lambar zinariya.

Bugu da kari kuma, a gun gasar wasan lankwashe jiki a kan dabe ta maza, Zou Kai na kasar Sin ya samu wata lambar zinariya.

A waje daya kuma, a gun gasar wasan takobi ta maza ta kungiya-kungiya da aka yi a wannan rana da maraice, kungiyar 'yan wasa ta Faransa ta lashe kungiyar Amurka, kuma ta samu wata lambar zinariya.

Sannan kuma, a gun gasar wasan tennis ta mutum-mutum ta maza, Rafael Nadal na kasar Spain ya lashe Fernando Gonzalez na kasar Chile ya samu wata lambar zinariya.

Haka kuma, a gun gasar Vault ta maza da aka gama dazun nan, Xiao Qin na kasar Sin ya samu wata lambar zinariya. Sakamakon haka, ya zuwa yanzu yawan lambobin zinariya da kasar Sin ta samu ya riga ya kai 32.

Sannan a gun gasar kwallon tebur ta mata ta kungiya-kungiya, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar Singapore ta samu wata lambar zinariya. Wannan ne karo na farko da kungiyar 'yan wasa ta mata ta kasar Sin ta samu lambar zinariya a gun wannan gasa. (Sanusi Chen)