Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:48:50    
Labarai na gasanni na kwana ta 6

cri

Zhang Juanjuan

Yau ran 14 ga wata, wata rana ce ta 6 da bude gasar Olympic ta Beijing. Ya zuwa karfe 9 na dare na wannan rana bisa agogon Beijing, an riga an fitar da lambobin zinariya 14.

A gun gasar karshe ta iyon kwado ta maza ta mita 200, Kosuke Kitajima, dan wasan kasar Japan ya samu lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajikinta na wasannin Olympic. Mr. Brenton Richard, dan wadan kasar Australiya da Duboscq Hugues, dan wasa na kasar Faransa sun samu lambobin azurga da tagulla.

A gun gasar karshe ta iyon da ake kira "malam-bude-littafi" ta mata ta mita 200, Liu Zige, 'yar wasa ta kasar Sin ta samu lambar zinariya. Kuma ta karya matsayin bajinta na duniya. Wannan ce lambar zinariya ta farko da kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin ta samu a gun gasar ninkayya ta wannan gasar wasannin Olympic. A waje daya, Jiao Liuyang, 'yar wasa ta kasar Sin daban ta samu lambar azurfa a gun gasar. Jessicah Schipper, 'yar wasa ta kasar Australiya wadda ta taba kafa matsayin bajinta na duniya ta samu lambar tagulla.

Haka kuma, a gun gasar iyon Freestyle ta maza ta mita 100, Bernard Alain, dan wasa na kasar Faransa ya samu lambar zinariya. Sullivan Eamon, dan wasa na kasar Australiya ya samu lambar azurfa, Lezak Jason na kasar Amurka da Cielo Filho na kasar Brazil su biyu sun samu lambar tagulla tare.

Bugu da kari kuma, a gun gasar iyon ba da sanda na Freestyle ta mata, kungiyar 'yan wasan iyo ta mata ta Australiya ta samu lambar zinariya, kungiyar 'yan wasan iyo ta mata ta kasar Sin ta samu lambar azurfa. Kungiyar 'yan wasan iyo ta mata ta kasar Amurka wadda ta samu lambar zinariya har sau 3 a gun gasannin Olympic ta samu lambar tagulla.

Sannan kuma, a gun gasar harbi ta mata ta mita 50 da 'yan wasa suke yi ta hanyoyi 3, Du Li, 'yar wasa ta kasar Sin ta samu lambar zinariya. Emmons Katerina ta kasar Czech wadda ta samu lambar zinariya ta farko ta wannan gasar Olympic ta samu wata lambar azurfa. Cruz Eglis Yaima ta kasar Cuba ta samu lambar tagulla.

Haka kuma, a gun zagaye na karshe na gasar lankwashe jiki na salo na maza, Yang Wei na kasar Sin ya samu lambar zinariya. Uchimura Kohei na kasar Japan ya samu lambar azurfa, sannan Caranobe Benoit na kasar Faransa ya samu lambar tagulla.

A gasar harbin faifai da bindiga daga fannoni biyu ta mata, 'yar wasa ta kasar Italiya Cainero Chiara ta samu lambar zinariya. 'Yar wasa ta kasar Amurka Rhode Kimberly ta samu lambar azurfa. 'Yar wasa ta kasar Jamus Brinker Christine ta samu lambar tagulla.

A gasar kokawa irin ta gargajiyar Roma ta maza ta ajin kilo 84, 'dan wasa na kasar Italiya Andrea Minguzzi ya samu lambar zinariya. 'Dan wasa na kasar Hungary Zoltan Fodor ya samu lambar azurfa.

A gasar harbi da kibiya ta mace dai dai, 'yar wasa ta kasar Sin Zhang Juanjuan ta samu lambar zinariya.

A gasar judo ta mata ta ajin kilo 78, 'yar wasa ta kasar Sin Yang Xiuli ta samu lambar zinariya.

A gasar judo ta maza ta ajin kilo 100, 'dan wasa na kasar Mongoliya Naidan Tuvshinbayar ya samu lambar zinariya, wannan ce lambar zinariya ta farko da kungiyar kasar ta samu a gun gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a halin yanzu.

A gasar kokawa irin ta gargajiyar Roma ta maza ta ajin kilo 96, 'dan wasa na kasar Rasha Aslanbek Khushtov ya samu lambar zinariya.

A gasar kokawa irin ta gargajiyar Roma ta maza ta ajin 120, 'dan wasa na kasar Cuba Mijain Lopez ya samu lambar zinariya.

A gasar takobi da ake ratayawa kan kugu ta mata tsakanin kungiya da kungiya, kungiyar kasar Sin ta samu lambar azurfa, kungiyar Ukraine ta samu lambar zinariya, wannan ce lambar zinariya ta farko da kungiyar kasar ta samu a gun gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a halin yanzu.(Danladi)