Chen Ying a tsakiya
Yau ranar 13 ga wata, an shiga kwana na biyar da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 17 a cikin gasannin da aka yi a yau. Ya zuwa karfe 9 na dare na wannan rana bisa agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya guda 15.
A ran 13 ga wata da safe, kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta mata ta kasar Sin ta lashe lambar zinariya wadda ta zama lambar zinariya ta farko da kasar Sin ta samu cikin wannan gasa a tarihi. Kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Amurka ta zama ta biyu. Kungiyar 'yan wasa na kasar Ramania ta zama na uku.
A gasar daukar nauyi na mata na ajin kilo 69, 'yar wasa ta kasar Sin Liu Chunhong ta samu lambar zinariya, kuma ta karya matsayin bajimtar duniya.
A gasar tsuduma cikin ruwa daga kan katako na tsayin mita uku na maza biyu biyu, 'yan wasa na kasar Sin Wang Feng da Qin Kai sun samu lambar zinariya.
A gasar harbe-harbe fistole na mita 25 na mata, 'yar wasa ta kasar Sin Chen Ying ta samu lambar zinariya.
A gasar kokawa na zamanin da na maza na ajin kilo 74, 'dan wasa na kasar Sin Chang Yongxiang ya samu lambar azurfa.
A cikin gasannin iyo, 'yar wasa ta kasar Australia Rice Stephanie ta samu lambar zinariya ta gasar iyo mai salo daban-daban na mutun daya ta mata ta mita 200, kuma ta karya matsayin bajimtar duniya da ta taba samu da kanta. 'Dan wasan kasar Amurka Phelps Micheal ya samu lambar zinariya ta gasar iyon da ake kira "Mallam-bude-littafi" ta maza ta mita 200, kuma ya karya bajimtar duniya. 'Yar wasan kasar Italiya Pellegrini Federica ta samu lambar zinariya cikin gasar iyo cikin 'yanci ta mata ta mita 200 tare da karya bajimtar duniya.
Ban da haka kuma, a cikin gasar iyo cikin 'yanci ta yada kanin wani ta maza ta mita 200 na mutane hudu-hudu, kungiyar 'yan wasan kasar Amurka da Phelps ya shugabanta ta samu lambar zinariya da mintoci 6 da dakika 58.56, kuma ta karya bajimtar duniya.
A gasar tseren keke kan tituna bisa tsawon lokaci ta mata, 'yar wasa ta kasar Amurka Armstrong Kristin ta samu lambar zinariya da mintoci 34 da dakika 51.72.
A gasar tseren keke kan tituna bisa tsawon lokaci ta namiji dai dai, 'dan wasa na kasar Switzerland Cancellara Fabian ya samu lambar zinariya.
A gasar judo na maza na ajin kilo 90, 'dan wasa na kasar Georgia Tsirekidze Irakli ya samu lambar zinariya. 'Yar wasa ta kasar Japan ta samu lambar zinariya a gasar judo na mata na ajin kilo 70.
A gasar kokawa irin ta gargajiyar Roma ta maza na ajin kilo 74, 'dan wasa na kasar Georgia Kvirkelia Manuchar ya samu lambar zinariya. 'Dan wasa na kasar Faransa Guenot Steeve ya samu lambar zinariya a gasar kokawa irin ta gargajiyar Roma ta maza na ajin kilo 66, wannan ce lambar zinariya ta farko da kungiyar kasar Faransa ta samu a gasar wasannin Olympics ta Beijing.
A gun gasar daukar nauyi na maza na ajin kilo 77, 'dan wasa na kasar Korea ta kudu Sa Jae-Hyouk ya samu lambar zinariya, 'dan wasa na kasar Sin Li Hongli ya samu lambar azurfa.(Danladi)
|