Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:48:21    
Labarai na gasanni na kwana ta 4

cri

Wang Xin da Chen Ruolin

Yau ranar 12 ga wata, an shiga kwana na hudu da soma gasar wasannin Olympics ta Beijing, gaba daya za a samu lambobin zinariya guda 19 a cikin gasannin da aka yi a yau. Ya zuwa karfe 9 na dare na wannan rana bisa agogon Beijing, an riga an samu lambobin zinariya guda 17. Kasar Sin ta samu lambobin zinariya 4.

A ran 12 ga wata da safe, kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Sin ta lashe lambar zinariya wadda ta taba rasawa kafin shekaru 4. Kungiyar 'yan wasan lankwashe jiki ta kasar Japan wadda ta taba samun lambar zinariya a gasar Olympic ta Athens ta zama ta biyu. 'kungiyar 'yan wasa na kasar Amurka ta zama ta uku.

A gun gasar iyo cikin 'yanci na tsawon mita 200 na maza, 'dan wasa na kasar Amurka Phelps na kasar Amurka ya samu lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajimtar duniya. Wannan ce lambar zinariya ta uku da ya samu a gasar Olympic ta Beijing.

A cikin gasar iyon kwado ta mata ta mita 100, 'yar wasan kasar Australia Jones Leisel ta samu lambar zinariya.

A cikin gasar wasan iyon rigingine ta maza ta mita 100, 'dan wasan kasar Amurka Peirsol Aaron ya samu lambar zinariya tare da karya bajimtar duniya.

A cikin gasar wasan iyon rigingine ta mata ta mita 100, 'yar wasa ta kasar Amurka Coughlin Natalie ta samu lambar zinariya.

Ban da haka kuma, 'dan wasan kasar Korea ta kudu Jin Jong Oh ya samu lambar zinariya a gasar harben sannu a hankali da karamin bindiga na mita 50 na maza. Tsohon 'dan wasan kasar Sin Tan Zongliang ya sami lambar tagulla.

A gasar tsunduma cikin ruwa daga dandali na tsayin mita 10 na mata biyu biyu, 'yan wasa na kasar Sin Wang Xin da Chen Ruolin sun samu lambar zinariya.

A gasar harbin faifai da bindiga daga fannoni daban daban na maza, 'dan wasa na kasar Amurka Eller Walton ya samu lambar zinariya, kuma ya karya matsayin bajinta na gasar wasannin Olympics.

A gasar daukar nauyi na ajin kilo 63 na mata, 'yar wasa ta kasar Korea ta arewa Pak Hyon Suk ta samu lambar zinariya.

A gasar kwale-kwale na Canoe Slalom tsakanin namiji dai dai, 'dan wasa na kasar Slovak Martikan Michal ya samu lambar zinariya. A gasar kwale kwale na Kayak Slalom tsakanin namiji dai dai, 'dan wasa na kasar Jamus Alexander Grim ya samu lambar zinariya.

A gasar kokawa na zamanin da na maza na ajin kilo 55, 'dan wasa na kasar Rasha Mankiev Nazyr ya samu lambar zinariya.

A gasar judo na mata na ajin kilo 63, 'yar wasa ta kasar Japan Tanimoto Ayumi ta samu lambar zinariya.

A gasar judo na maza na ajin koli 81, 'dan wasa na kasar Jamus Bischof Ole ya samu lambar zinariya.

A gasar takobin da ake ratayawa a kugu na namiji dai dai, 'dan wasa na kasar Sin Zhong Man ya samu lambar zinariya.

A gasar daukar nauyi na maza na ajin kilo 69, 'dan wasa na kasar Sin Liao Hui ya samu lambar zinariya.(Danladi)