Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-21 20:48:08    
Labarai na gasanni na kwana ta 3

cri

Zhang Xiangxiang

Yau, wato ran 11 ga wata, an shiga kwana na uku da soma gasar Olympic ta Beijing. An riga an samu dukkan lambobin zinariya 13 a gasar. An karya matsayin bajinta na duniya har sau 3 a gasannin ninkaya.

Kungiyar 'yan wasan ninkayya maza ta kasar Amurka ta samu lambar zinariya a gun gasar wasan tseren ninkayya na mita dari-dari na 'yan wasa 4 , kuma an yanke matsayin bajinta na duniya. A gun gasar ninkaya ta mita dari 1, Mr. Kitajima Kosuke, sarkin ninkaya na kasar Japan ya samu wata lambar zinariya, kuma ya yanke matsayin bajinta. A gun gasar kusa da ta karshe ta iyon rigingine, 'yar wasa ta kasar Zimbabuwei Kirsty Coventry ta karya matsayin bajinta na duniya.

A gun gasar harbe harbe na kungiyar maza, kungiyar kasar Korea ta kudu ta samu lambar zinariya.

A gun gasar tsunduma cikin ruwa daga kan dandali na tsayin mita 10 na maza biyu biyu, 'yan wasa na kasar Sin Lin Yue da Huo Liang sun samu lambar zinariya. A gun gasar daukar nauyi na ajin kilo 58 ta mata, 'yar wasa ta kasar Sin Chen Yanqing ta samu lambar zinariya, haka kuma ta karya matsayin bajinta na duniya.

Sa'an nan kuma Bindra Abhinav, dan wasan harbi na kasar Indiya ya samu wata lambar zinariya a gun gasar harbi ta maza ta mita 10. Wannan ne lambar zinariya ta farko da kasar Indiya ta samu a gun gasar Olympic.

Bugu da kari kuma, madam Trickett Lisbeth, 'yar wasan ninkayya ta kasar Australiya ta samu wata zinariya a gun gasar wasan ninkayya ta malam-bude-littafi ta mita dari 1 a gun gasar Olympic ta Beijing. Sannan Adlington Rebecca, 'yar wasan ninkayya ta kasar Britaniya ta samu wata lambar zinariya ta mita dari 4. 'Yar wasa ta kasar Finland Makela-Nummela Satu ta samu lambar zinariya a gun gasar harben bindiga daga fannoni daban-daban ta mata.

A gun gasar daukar nauyi na maza na ajin kilo 62, 'dan wasa na kasar Sin Zhang Xiangxiang ya samu lambar zinariya.

A gun gasar judo na maza na ajin kilo 73, 'dan wasa na kasar Azerbaijan Elnur Mammadi ya samu lambar zinariya, wannan lambar zinariya ta farko ce da kungiyar wakilai ta kasar Azerbaijan ta samu a gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a halin yanzu.

A gasar takobi maras nauyi kuma gajere na mutum dai dai, 'yar wasa ta kasar Italiya Vezzali ta samu lambar zinariya.

Ban da wannan, a ran 11 ga wata, kwamitin Olympic na kasa da kasa ya sanar da cewa, an gano maganin EPO, wani maganin sa kuzari daga jikin Moreno Maria, wata 'yar wasan tseren keke ta kasar Spain. Sakamakon haka, an kori Moreno Maria daga gasar Olympic ta Beijing.(Danladi)