Long Qingquan
Yau ranar 10 ga wata, an shiga kwana na biyu da gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing, ya zuwa karfe 9 na dare, gaba daya aka samu lambobin zinariya guda 13.
A ranar 10 ga wata da safe, 'dan wasan iyo na kasar Amurka Michael Phelps ya karya matsayin bajimta na duniya kuma ya samu lambar zinariya a gasar iyo mai salo daban-daban na mita 400 na maza.
Haka kuma 'dan wasan iyo na kasar Korea ta kudu Park Taehwan ya samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 41.86 a gun gasar iyo cikin 'yanci na mita 400 na maza. 'Dan wasan iyo na kasar Sin Zhang Lin ya samu lambar azurfa a gasar, wadda ta zama lamba ta farko da 'yan wasa maza na kasar Sin suka samu a gun gasannin iyo na wasannin Olympics.
A gun gasar mai salo daban-daban na mita 400 na mata, 'yar wasa ta kasar Australiya Stephanie Rice ta karya matsayin bajimta na duniya kuma ta samu lambar zinariya da mintoci 4 da dakika 29.45.
A gun gasar iyo cikin 'yanci na yada kanin wani na tsawon mita dari-dari na mata hudu-hudu, kungiyar kasar Holland ta samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 33.76 a yau da safe.
A gasar harbe-harben fistole na mita 10 na mata, 'yar wasa ta kasar Sin Guo Wenjun ta samu lambar zinariya da zobba 492.3.
A cikin gasar taka tsalle cikin ruwa mai katako na tsayin mita uku na mata, 'yan wasa na kasar Sin Guo Jingjing da Wu Minxia sun samu lambar zinariya.
A gun gasar harbe harben bindiga daga fannoni daban-daban na maza, 'dan wasa na kasar Czech Kostelecky David ya samu lambar zinariya.
A gun gasar daukan nauyi na ajin kilo 53, 'yar wasa ta kasar Thailand P. Jaroenrattanatarakoon ta samu lambar zinariya. A gun tseren keke kan hanyar mota ta mata, 'yar kasar Ingila Nicole Cooke ta samu lambar zinariya.
A gun gasar harba kibiya da aka shirya a ran 10 ga wata, kungiyar mata ta kasar Korea ta kudu ta samu lambar zinariya, kungiyar mata ta kasar Sin ta zo ta biyu a gun gasar.
A gasar judo ta mata ta ajin kilo 52, 'yar wasa ta kasar Sin Xian Dongmei ta samu lambar zinariya.
A gasar judo ta maza ta ajin kilo 66, 'dan wasa na kasar Japan Uchishiba Masato ya samu lambar zinariya.
A gasar daukar nauyi ta ajin kilo 56 da aka gama ba da dadewa ba, 'dan wasa na kasar Sin Long Qingquan ya samu lambar zinariya, wannan dai lambar zinariya ta 6 ce da kasar Sin ta samu a gasar wasannin Olympics ta Beijing da ake gudanarwa.(Danladi)
|