"Barka da zuwa! Nan cibiyar ba da agajin gaggawa ta asibitin birnin Beijing mai wayar lamba 120, ko kana bukatar wani taimako? Ko kana bukatar motar ba da agajin gaggawa ta asibiti, a shirye muke za mu tura motar,sai ka yi hakuri ka yi jira, mene ne kake fama da shi?"
Maganar da kuka ji dazu,Magana ce da mallama Luo Xiaojing,'yar sa kai da ke iya Magana da harshen Spanish ta yi yayin da ta ke cikin shirin aiki a cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing mai wayar lamba 120, tana Magana da wani mutum da ya shiga burtun bakon spain wanda yake neman taimako.
Da aka fara wasannin Olympics a birnin Beijing ana bukatar kwararru masu iya Magana da harsuna da yawa na kasashen waje. Tun daga karshen shekara ta 2006 ne cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing mai wayar lamba 120 ta fara daukar mutane masu iya Magana da harsunan waje duk domin bad a hidima ga baki masu yawon shakatawa da 'yan wasa na kasashen waje yayin da ake yin wasannin Olympics a nan birnin Beijing.wadannan mutanen da aka dauka dukkansu masu aikin sa kai ne. Bisa jagorancin da likitocin cibiyar suka yi musu,ma'aikata masu sa kai sun yi atisayen ayyukan ba da agajin gaggawa,kamar su amsa wayoyin neman taima da baki, da yi mu'amala da su da kuma biya bukatunsu,sun kuma ba da taimakonsu ga likitocin cibiyar wajen ayyukan yau da kullum.
Malama Luo Xiaojing tana daya daga cikin ma'aikata masu sa kai dake iya Magana da harsunan waje da cibiyar bad a agajin gaggawa ta birnin Beijing ta dauka, aikinta shi ne amsa wayoyi da mutane masu yaren Spain dake neman taimako za su yi a lokacin wasannin Olympics a nan birnin Beijing. Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta shiga aikin sa kai a cibiyar ba da agajin gaggawa ta birnin Beijing, malama Luo Xiaojing ta bayyana cewa" bayan da na kammala karatuna a jami'a ina aiki a ma'aikatun kiwon lafiya, na yi aiki tare da likitoci cikin shekaru uku a kasashen waje, wasu kalmomin da ake amfani da su a fannin likitanci ko na sinanci ko na spainish na saba da su, ina tsammani babu matsala gare ni wajen amsa wayoyin baki. Zan iya sauke nauyin da ke bisa wuyana da kwarewata a harshen Spain.
A kan matsayin dan sa kai,wani dalibin dake koyon harshen Japananci a jami'ar koyon harsunan waje ta biyu ta birnin Beijing mai suna Sun Peng yana mai ra'ayin cewa amsa wayoyin neman taimako a cibiyar ba da taimakon gaggawa ta birnin Beijing mai wayarlamba 120 ba aiki mai sauki ban e,ba ma kawai yana bukatar ka kware a harshe ba har ma ya kamata kana da wasu ilimi game da likitanci,babbar jarabawa gare ni.ya ce ya niyyata zai dauki wannan nauyi.Ya ce "wasannin Olympics na shekara ta 2008,wata muhimmiyar dam ace. A hakika ina so in shiga dukkan ayyukan sa kai. Ayyukan ba da taimakon gaggawa na cibiyar ba da agajin gaggawa mai wayar lamba 120 wani batu ne mai muhimmancin gasket, a ganina shiga ayyukan sa kai tana da amfani sosai, na iya taimaka mutane masu Karin yawa."
Da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya duba takardun sunayen, ya ga shekarunsu sun sha banban,, yayin day a ke Magana da su,ya ga ko kwararru tsofaffi ko samari masu kuruciya,dukkansu sun bayyana burinsu na shiga ayyukan sa kai da ba da taimakonsu ga wasannin Olympics na Beijing. (za a cigaba)
|