Ranar 10 ga wata, ranar farko ta gasar karshe ce wajen gasar iyo ta wasannin Olympics na Beijing. A wannan rana da safe, 'dan wasa na kasar Sin Zhang Lin, ya samu lambar azurfa a gasar iyo cikin 'yanci ta mita 400, haka kuma, ya zama 'dan wasan iyo na farko na kasar Sin wajen samun lambar yabo a gun wasannin Olympics.
A gasar karshe, Zhang Lin, 'dan shekaru 21 daga birnin Beijing ya nuna kwarewa sosai a karshen mita 50, har ma ya wuce wasu shahararrun 'yan wasa daga kasashen Australia, da Amurka, da dai sauransu, a karshe dai 'dan wasa na kasar Korea ta kudu ya lashe shi da kankancin rinjaye. Amma, ko da yake haka, Zhang Lin ya bude sabon shafi na tarihin iyo na maza na kasar Sin. Kafin wannan kuma, matsayi na hudu shi ne sakamakon da ya fi kyau da 'yan wasan iyo na maza na kasar Sin suka samu a wasannin Olympics, kuma wannan ne abu a shekaru 12 da suka wuce. Bayan gasar, Zhang Lin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Lallai ina jin farin ciki sosai, a ganina, na samu wannan lambar yabo, wannan cimma tudun dafawa ne da muka yi. Ina fatan kungiyar 'yan wasan iyo ta kasar Sin, da dukkan kungiyar wakilai ta kasarmu, za su samu sakamako mafi kyau bisa na wasannin Olympics na karo da ya wuce."
Yanzu, kungiyar 'yan wasan iyo ta maza ta Asiya ta riga ta zama wani rukunin da ba a iya kasa kula da ita ba a wasan iyo. 'Yan wasa daga kasashen Japan, da Korea ta kudu sun riga sun zama zakarun wasannin Olympics, haka kuma ya matsa wa kungiyar 'yan wasan iyo ta kasar Sin sosai. Domin cimma tudun dafawa a wasannin Olympics na Beijing, Zhang Lin ya taba je kasar Australia har sau biyu a shekarar da ta wuce, da shekarar bana, kuma ya samu horo daga wani shahararren mai horar da 'yan wasan iyo na kasar. A sakamakon haka, ya samu cigaba sosai a rabin shekarar da ta wuce, har ma sau da yawa ya karya matsayin bajinta na kasa da na Asiya, haka kuma ana sa rai kan da'irar wasannin iyo. Zhang Lin, wanda a karo na biyu ne ya halarci wasannin Olympics, ya gaya wa wakilinmu cewa, dalilin da ya sa ya samu narasa shi ne, domin kyakkyawar hadin gwiwar da ke tsakaninsa da mai horar da 'yan wasa na kasaar Australian, da na kasar Sin. Ya ce, "Mun kafa wata karamar kungiya ce da ke hade da ni, da mai horar da ni na Sin da na Australian. Gaskiya ne wannan lambar yabo tana da ma'ana sosai, ba ni daya kawai ke iya samunta ba."
A cikin zaman rayuwarsa, Zhang Lin na son kallon majigin yara, da wasan kamputa. Amma, idan ya shiga wurin waha, to, nan da nan ya kasance mai karfi sosai. Mai sharhi kan motsa jiki na gidan talibijin na kasar Slovakia Stainislav ya ce, "Gasar gasar iyo cikin 'yanci ta mita 400 gasar fid da gwani ce. Na yi mamaki sosai saboda 'dan wasa na kasar Korea ta kudu ya samu nasara a gasar, amma abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, 'dan wasa na kasar Sin Zhang Lin ya samu lambar azurfa, gaskiya ne ya nuna kwarewa sosai a gasar."
A gun wasannin Olympics na Beijing, Zhang Lin zai shiga gasar iyo cikin 'yanci ta mita 1500, da gasar iyon ba da sanda cikin 'yanci. Muna fatan zai cigaba da samun sakamako mai kyau.
|