Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-20 20:39:02    
'Yan mata masu sa kaimi ga 'yan wasa a kan rairayi

cri

Sabo da hasken rana da rairayi da 'yan wasa masu kyan kira, shi ya sa wasan kwallon raga a kan rairayi yana daya daga cikin wasannin da ya fi jawo hankulan mutane. A filin wasan na gasar wasannin Olympics ta Beijing, 'yan mata fiye da 30 masu sa kaimi ga 'yan wasa da suka zo daga kasar Spain da biranen Guangzhou da Beijing na kasar Sin su ma sun jawo hankulan mutane sosai. Amma a hakika dai, domin ba da hidima ga wasannin Olympics da kuma kawo wa 'yan kallo da kuma su kansu farin ciki, wadannan 'yan mata sun ji gajiya sosai da kuma yi hakuri da kasa kallon wasannin Olympics. To yanzu ga cikakken bayani.

A filin wasan kwallon raga a kan rairayi, 'yan mata masu sa kaimi ga 'yan wasa da ke da kyaun gani kwarai da gaske sun jawo hankulan 'yan kallo sosai, amma mutane kakilan ne suka san wahalolin da suka sha kafin sun nuna wasan fasaha. Wurin da 'yan mata 17 daga birnin Guangzhou da kasar Spain suke zama a wani daki ne da fadinsa bai kai murabba'in mita 30 ba da ke cikin wurin shan iska na Chaoyang inda ake yin wasan. Sabo da babu talijibin da Internet, ba yadda za a yi sai sun samu labarai kan yawan lambobin zinariya da kasar Sin ta samu daga sauran mutane. Wang Xue'er, wata mace mai sa kaimi ga 'yan wasa ta gaya mana cewa,

"A wasu lokuta, ban san lambobin zinariya nawa da kasar Sin ta samu a cikin wasannin Olympics ba, ba yadda zan yi sai na tambayi sauran mutane. Akwai talibiji daya kawai a dakin cin abinci, shi ya sa a wasu lotuka mun je can don kallon gasanni."

Har kullum kungiyar masu sa kaimi ga 'yan wasa mai suna "yin raye-rayen zamani" da ta zo daga birnin Guangdong ta kan sa kaimi ga 'yan wasan kwallon kwando na kasar Sin, amma a wannan karo, sun gudanar da aikin sa kaimi ga 'yan wasan kwallon raga a kan rairayi. Domin sabawa da rairayi mai laushi, membobin kungiyar su kan yin horaswa har na tsawon sa'o'i 7 a ko wace rana. Wang Xue'er, shugabar kungiyar ta bayyana cewa, yin raye-raye a kan rairayi wani babban kalubale ne ga 'yan kungiyar. Kuma ta kara da cewa, "Ban iya nuna karfi sosai lokacin da nake yin raye-raye a kan rairayi. Ya kamata a sarrafa da kafafu sosai, in ba haka ba za a fadi, shi ya sa tabbas ne a mai da hankali kwarai da gaske."

Ko da yake a kan sha wahala sosai wajen horaswa da kuma nuna wasan fasaha, amma 'yan mata masu sa kaimi ga 'yan wasa su ma suna da lokacin faranta ransu. A ran 11 ga wata, Kobe Bryant, sanannen tauraro na wasan kwallon kwando na kasar Amurka wato NBA ya je wurin shan iska na Chaoyang don kallon wasan kwallon raga a kan rairayi. Wadannan 'yan mata sun yi murna kwarai da gaske da ganin abin gunki da ke cikin zukatansu. Kuma Wang Xue'er ta bayyana cewa,

"Dukkanmu mun fadi cewa, Kobe ya zo, Kobe ya zo. Gaskiya ne muna son daukar hotuna tare da shi, amma sabo da aiki, ba mu iya fito ba."

Ko da yake 'yan mata masu sa kaimi ga 'yan wasan kwallon raga a kan rairayi sun sha wahala da kuma jin dadin zaman rayuwarsu, amma ba wadda ta yi koke-koke ba. Wang Xue'er ta ce, ba a iya auna aikinsu da kudade ba, dalilin da ya sa haka shi da sabo da dukkansu suna da wani buri.

"Burinmu shi ne nuna kanmu a gun gasar wasannin Olympics, da kuma nuna irin wannan kyan ganinmu da kuma ruhun sa kaimi ga 'yan wasa ga 'yan kallo, ta yadda za a iya kara jin dadin wasan."

To, masu sauraro, shirinmu na yau na "Labaru masu ban sha'awa kan wasannin Olympics" ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)