Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-20 15:33:15    
Masu sha'awar motsa jiki na kasar Kenya sun yi mamaki da farin ciki kan lambobin zinariya guda biyu da 'yan wasa na kasar suka samu a rana daya

cri

A ranar 18 ga wata a gun gasar gudu da ketare shinge ta mita 3000 ta maza, da gasar karshe ta mita 800 ta mata na wasan guje guje da tsalle tsalle a wasannin Olympics na Beijing, 'yan wasa daga kasar Kenya sun samu lambobin zinariya guda biyu, a waje daya kuma, sun samu lambobin tagulla da na azurfa a wasannin biyu. Wato a cikin wadannan gasanni biyu da suke da nisan mintoci 20, kungiyar wakilai ta kasar Kenya ta samu lambobin zinariya guda biyu, da lambar azurfa guda daya, da lambar tagulla guda daya, haka kuma masu sha'awar motsa jiki na kasar Kenya sun nuna ban mamaki kan wannan. Wakilanmu da ke birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya sun yi farin ciki tare da su, yanzu kuma bari mu ga cikakken bayanin da suka ruwaito mana daga Kenya:

Ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 2008, rana ce da ke da ma'ana sosai ga kasar Kenya da ke gabashin Afrika, a gasar gudu da ketare shinge ta maza ta mita 3000, Brimin Kiprop Kipruto, 'dan wasa daga kasar Kenya ya samu lambar zinariya, 'dan wasa daban na wannan kasa Richard Mateelong ya samu lambatiri. A gun gasar karshe ta mita 800 ta mata da aka shirya bayan gasar ba da dadewa ba, Pamela Jelimo, 'yar wasa mai shekaru 18 kawai ta kara samun lambar zinariya ga kasar Kenya, abokiyarta Janeth Jepkosgei Busienel ta zo na biyu.

Gasannin biyu gasannin da 'yan wasan kasar Kenya suke kwarewa a kai. Ko da ya ke a ran Litinin ne aka shirya gasannin biyu, amma mutanen kasar Kenya da yawa sun dakatar da ayyukansu, kuma suna kallon talibijin, don jiran wannan lokaci mai tsuma jiki. Wakilanmu sun kai ziyara a wani kulob na motsa jiki da ke birnin Nairobi, don kallon gasannin da aka bayar kai tsaye.

A lokacin kusan karewar gasar gudu da ketare shinge ta mita 3000 ta maza, ba zato ba tsamani Kipruto ya soma yin tsarto na karshe, a sakamakon haka, ya zama zakara da minti 8 da dakika 10 da 34.



A lokacin da ake jin farin ciki da tsuma saboda lambar zinariya ta farko da aka samu, bayan minti 20 da suka wuce, Pamela Jelimo ta zama zakara a gasar mita 800 ta mata da gagarumin rinjaye. Janeth Jepkosgei Busienei ta samu lambar azurfa.
Mutanen da ke kulob suna runguma da juna tare. Har ma mai horar da 'yan wasan kwallon tennis Sebit Mohammed ya yi tsalle daga kujera, ya ce,

"Jikina ya tsumu sosai, mun kara samun wata lambar zinariya. Yanzu kuma, ban da farin ciki, babu sauran maganganun da ke iya nuna abin da nake ji. Lallai wannan rana ce da na fi jin farin ciki. Na yi alfarma ga kasarmu."
Judy Achieng, mai aiki a kulob, ta ce, 

"'Yan wasan kasarmu sun samu lambobin zinariya guda biyu a rana daya, gaskiya ne suna da kwarewa sosai. Idan akwai dama, zan yi maraba da su a lokacin da suke komawa."

Ban da wadannan lambobin zinariya guda biyu kuma, ana kyautata zaton za a samu lambobin yabo a gasar mita 5000 ta maza da ta mata, da kuma gasar gudun dogon zango wato Marathon ta maza. Muna fatan 'yan wasan kasar Kenya za su kara samun nasara a wasanni masu zuwa.