Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-20 09:03:27    
Jama'ar Holand sun ba da taimakon kudi domin shirya gasar wasannin Olympic

cri

Bisa yarjejeniyar da aka daddale, an tsai da cewa za a shirya zama na 9 na gasar wasannin Olympic ta shekarar 1928 a birnin Amsterdam na kasar Holand. Amma yayin da ake yin kokarin share fage, an ji muryar nuna kiyayya.

Wasu 'yan majalisar dokoki na kasar Holand sun nuna shakka cewa, ko ya yi daidai birnin Amsterdam ya dauki bakuncinsa domin gasar wasannin Olympic, kuma sun kai suka ga gwamnatin kasarsu saboda ba ta mai da hankali kan aikin warware matsalolin da jama'ar kasar ke fuskanta ba, alal misali aikin kyautata sharadin gidajen kwana da na sufuri da dai sauransu. Ban da wannan kuma, wasu sun bayyana cewa, kuzarin wasannin motsa jiki ya sa 'yan mata su rasa ladabi, suna ganin cewa, bai kamata ba 'yan mata su halarci gasar wasannin Olympic.

A sanadiyar haka, majalisar dokokin Holand ta ki yarda ga gwamnatin kasar da ta samar da kudin shirya gasar wasannin Olympic, haka kuma aikin shirya gasar wasannin Olympic ta Amsterdam ya shiga hali mai tsanani, kuma shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Amsterdam ya ga tilas ya yi murabus daga mukaminsa. Dukkan wadannan sun sa hankalin yawancin mutanen kasar ya tashi saboda suna goyon bayan birnin da ya shirya gasar wasannin Olympic.

A karkashin irin wannan hali, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na birnin Amsterdam ya nemi dukkan jama'ar kasar Holand da su gabatar da kudin taimako domin shirya gasar wasannin Olympic. Don tabbatar da shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 1928 lami lafiya, jama'ar kasar Holand sun ba da kudin taimako bi da bi, bayan makonni biyu kawai, sai kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Amsterdam ya samu kudi fiye da kima. Don nuna godiya gare su, gwamnatin kasar Holand ta gina wani filin wasannin motsa jiki mai daukan 'yan kallo dubu 40, cibiyarsa ita ce filin wasan kwallon kafa, a kewayen cibiyar nan kuma, an gina dakunan wasannin motsa jiki tare da hanyoyin guje-guje. A wancen lokaci, filin ya kai matsayin koli a duniya.

A ran 28 ga watan Yuli na shekarar 1928, an yi bikin bude zama na 9 na gasar wasannin Olympic a birnin Amsterdam, a cikin sararin sama, ana iya ganin wuta mai launuka daban daban da aka harba, jiragen sama kuwa sun yi yawo a cikin sararin sama domin nuna fasahar musamman. 'Yan wasa da jami'ai mahalarta bikin da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 46 sun yabawa aikin kwamitin shirya gasar sosai da sosai, amma jama'ar Holand da suka ba da taimakon kudi su ne ainihin jarumai.(Jamila Zhou)