Ran 8 ga wata da tsakan dare, bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ya ci cikakkiyar nasara! Nune-nunen da aka yi a cibiyar wasan motsa jiki ta kasar Sin sun nuna wa jama'ar kasashen duniya azurtattun al'adun kasar Sin. Manyan siffofin kafa 29 da aka zana da kayan harbar wuta a cikin sararin sama na cibiyar Beijing sun kara nuna wa duk duniya karfin wasannin Olympic. Lokacin da tsohon 'dan wasan kasar Sin Li Ning ke kunna babbar wutar yula, sai aka sanar da cewa, zama ta 29 ta gasar wasannin Olympic wadda kirarinta shi ne 'duniya daya, buri daya' ta soma a hukunce.
'Yan kallo a duk fadin duniya sun yabawa wannan gaggarumin biki sosai da sosai, amma kila ne ba su san ainihin kokarin da ma'aikatan da abin ya shafa suka yi kafin wannan.
Rukunin sadarwa ta hanyar yanar gizo na kasar Sin wanda shi ne abokin hadin gwiwa wajen sadarwa na gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ma ya yi iyakacin kokarinsa. Game da wannan, kakakin watsa labarai na rukunin Li Litao ya yi mana bayani cewa, aikin hidima da rukunin sadarwa ta yanar gizo na kasar Sin yake gabatar wa bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ya fi inganci a tarihin wasannin Olympic. Li Litao ya ce: "Yan kallo sama da biliyan hudu dake kasashe da shiyyoyi 204 a duk fadin duniya sun kalli bikin bude gasar wasannin Olympic a gaban TV kai tsaye, rukunin sadarwa ta hanyar yanar gizo na kasar Sin ne ya shirya musu siginar TV bisa fasahar zamani, amma a da ba a taba yin amfani da irin wannan fasaha ba. Kamfanonin dillancin labaru da 'yan jaridan gidajen rediyo da jaridu da mujaloli daban daban na kasashen duniya sun yi amfani da tsarin yanar gizo da rukunin sadarwa ta yanar gizo na kasar Sin ya samar musu, sun watsa labarai ga duk duniya a wurin shirya bikin bude gasar cikin lokaci."
Don kara biyan bukatun 'yan kallo dake duk fadin duniya, rukunin sadarwa ta yanar gizo na kasar Sin ya sanya matukar kokarinsa. Li Litao ya kara da cewa, "A cikin awoyi biyar wato a gun bikin bude gasar wasannin Olympic, rukunin ya yi amfani da kumbunan sako 15 da sauran kayayyakin zamani, gaba daya ya gabatar da shirye-shiryen TV masu tsawon mintoci fiye da dubu 30. Ban da wannan kuma, tsarin sadarwa na kumbon sako na rukunin ya gabatar wa gidajen rediyo masu hoto 6 dake kasar Amurka da Hongkong da kasar Mexico da kasar Brazil da kasar Japan labaran TV kan bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing masu tsawon mintoci sama da dubu daya."
A sa'i daya kuma, rukunin ya samar wa 'yan jarida wani katin musamman na shiga internet, da haka suna iya yin aiki ta internet ko ina a ko da yaushe. Wannan shi ma sabuwar fasaha ce da ba a taba ganinta ba a tarihin wasannin Olimpic.
Ban da wannan kuma, wasan harbar wuta a gun bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ma ya ba mu babban mamaki, don tabbatar da aikin lami lafiya, rukunin sadarwa ta yanar gizo na kasar Sin ya kafa wani tsarin musamman don ba da umurni kan aikin. Li Litao ya gaya mana cewa: "Domin tabbatar da gudanarwar aikin lami lafiya, ma'aikatan rukuninmu sama da 100 sun tafi wurare daban daban tare da tsarin sadarwa na musamman, a karshe dai, mun ci cikakkiyar nasara."
A ran 8 ga wata da tsakan dare, babbar wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta kone sosai a sararin sama na filin wasan motsa jiki na kasar Sin wato 'bird's nest', cibiyar ba da umurni ta rukunin sadarwa ta hanyar yanar gizo na kasar Sin ta sami sako cewa, kome da kome suna tafiya yadda ya kamata. Hidimar da rukunin ya samar wa gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami cikakkiyar nasara.(Jamila Zhou)
|