Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-19 19:12:50    
Bayanin dakin wasan iyo na Yingdong

cri

A gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, za a yi gasar wasan kwallon ruwa da kuma gasar iyo da ke matsayin bangaren wasan Pentathlon na zamani a dakin wasan iyo na Yingdong da ke arewacin birnin Beijing.

Dakin wasan iyo na Yingdong dakin wasa ne da masu sha'awar iyo ke lakanta. A cikin wannan dakin wasan iyo, akwai wuraren wasan ninkaya masu fadi da na'urorin zamani da kuma kyakkyawan muhalli. Amma abu mafi muhimmanci shi ne tikitocin shiga wannan dakin wasa na da rahusa, shi ya sa har kullum dakin wasan iyo na Yingdong wuri ne mai kyau ga mazaunan Beijing domin gudun zafi a lokacin zafi.

An soma gina dakin wasan iyo na Yingdong a shekarar 1986. Marigayi Huo Yingdong, wani dan kasuwa na Hong Kong shi ne ya ba da kyautar kudin Hong Kong miliyan 100 domin gina wannan dakin wasa bayan da Beijing ta sami damar shirya taron wasannin motsa jiki na Asiya na shekarar 1990 wato a karo na 11. Shi ne dakin wasan iyo mafi girma a Asiya a lokacin. Bayan taron wasannin motsa jiki na Asiya a karo na 11, an sha yin muhimman gasannin iyo na kasa da kasa a wajen.

Don shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fara yin kwaskwarima da fadada dakin wasan iyo na Yingdong tun daga watan Afril na shekarar 2006, kuma ya kammala ayyukan a watan Satumba na wannan shekara. Bayan da aka fadada shi, fadin dakin wasan iyo na Yingdong ya kai misalin murabba'in mita dubu 43, inda ake da wurin wanka guda da aka kafa bisa ma'aunin duniya da wurin wasan ninkaya na horo daya da kuma na tsunduma cikin ruwa daga katako daya da kuma na dumamar jiki daya.

In an tabo magana kan dakin wasan iyo na Yingdong, ba za mu manta da marigayi Huo Yingdong ba. A matsayin dan kasuwa mai karfi, har kullum marigayi Huo ya nuna goyon baya kan bunkasuwar sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin. Shirya taron wasannin Olympic a kasar Sin burinsa ne da ya yi duk tsawon ransa yana neman cimmawa. A shekarun 1980, Beijing ta sami damar bakuncin taron wasannin motsa jiki na Asiya a karo na 11, amma saboda ayyukan gina dakuna da filayen wasa domin wannan muhimmin taron wasannin motsa jiki sun yi yawa, shi ya sa ana yi karancin kudi. A irin wannan lokaci ne marigayi Huo ya ba da dimbin kyautar kudi wajen gina dakin wasan iyo. Saboda haka ne muka sami dakin wasan iyo da muke gani a yau, wanda aka nada wa sunan wannan marigayi wato Yingdong.

A lokacin da Beijing take neman samun damar shirya taron wasannin Olympic, marigayi Huo ya taka babbar rawa. Ya taba ba da tasirinsa wajen shawo kan wakilan kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da su goyi bayan Beijing. Bugu da kari kuma, bayan da Beijing ta ci nasara, ya ba da kyautar kudin Sin yuan miliyan 200 domin gina dakin wasan iyo na kasar Sin, wanda ake bukatar kudin Sin yuan miliyan 800 domin gina shi.