Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 21:45:40    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Bisa wani labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar kwanan baya an ce, tun bayan da aka bude babban nuni mai sunan "Jihar Tibet ta yanzu da ta zamanin da" a ran 30 ga watan Afril a nan birnin Beijing zuwa yanzu, nunin ya jawo martani sosai daga wajen mutanen sassa daban-dabaan na zamantakewar kasar Sin, da akwai 'yan kallo wadanda yawansu ya kai dubu 110 sun kalli nunin. Bisa bukatar da tarin 'yan kallo suka gabatar, za a tsawaita lokacin yin nunin wanda da ma an yi shirin rufewarsa a ran 25 ga watan Yuli.

Cikin watanni 2 da 'yan kwanakin da suka wuce, wannan nuni kuma ya jawo hankulan aminanmu da yawansu ya wuce 1,000 wadanda suka zo daga kasashe 150 sun zo nan birnin Beijing don kalli nunin.

Wannan nuni kuma ya kasu kashi 2 wato "Tarihin jihar Tibet da tsarin bayi manoma na gargajiya" da "Sabuwar jihar Tibet wadda take yin sauye-sauye da wadata a kowace rana". Sashen kula da harkokin dunkulalliyar kungiyar gwagwarmaya ta kwamitin tsakiya na J.K.S., da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da kwamitin kula da harkokin kabilu na kasar, da kuma gwamnatin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta su ne suka shirya wannan nuni ta hanyar hadin gwiwa.

---- Kwanan baya a birnin New York na Amirka, yayin da madam Luise Blouin Macbain, mashahuriyar buga laittattafai ta kasashen duniya, kuma shugaban asusun Luise Blouin take ganawa da kungiyar wakilan masanan ilmin Tibet ta kasar Sin, ta bayyana cewa, a shirye take ta kafa asusun kasashen duniya domin kiyaye al'adun gargajiya na jihar Tibet, kuma za ta yi wa mutunen duniya bayani kan kokarin da kasar Sin ke yi wajen kiyaye al'adun gargajiya na jihar Tibet.

Madam Macbain ta ce, kasar Sin ta yi matukar kokari domin ba da kariya ga al'adun gargajiya na jihar Tibet, kuma ta yi shirin kara zuba kudin dala miliyan 70 cikin shekaru 5 masu zuwa domin wannan aiki. Sabo da kwarin gwiwar da ta samu daga wannan misali, shi ya sa ta tsai da kudurin kafa asusun musamman domin ba da kariya ga al'adun gargajiya na jihar Tibet.

Ban da wannan asusu kuma, madam Macbain ta yi shirin kafa wani sashen Tibet na musamman a gun taron shekara- shekara wato "taron koli na shugabannin kirkire-kirkire na duniya" wanda ita da kanta ta shirya, wanda kuma za a bude a watan Satumba na wannan shekarar da muke ciki, kuma za ta gayyaci shugabanni da masanan ilmi da abin ya shafa na kasar Sin da su yi bayanai kan halin da ake ciki a jihar Tibet. Ban da wannan kuma ta ba da shawara ga MDD da wasu kasashe da su shirya nune-nunen hotuna da kayayyakin jihar Tibet, ko kuma shirya wasu bukukuwan al'adun da abin ya shafa, ta yadda mutane wadanda sai kara yawa suke za su fahinci tarihi da halin da ake ciki yanzu da na nan gaba a jihar Tibet ta kasar Sin.