Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 20:53:09    
Gasar Olympic ta Beijing za ta zama gasar Olympic mafi kyau a kan tarihin gasannin Olympic, a cewar Muhammed Shahin

cri

Kasar Masar wadda take kan matsayin kasa mafi karfi wajen wasannin motsa jiki a cikin kasashen Larabawa da Afirka, ta aika da kungiyar wakilan wasannin motsa jiki da ke kunshe da membobi 177 zuwa gasar Olympic ta Beijing. A kwanan baya, malam Muhammed Shahin, shugaban kungiyar wakilan wasannin motsa jiki ta kasar Masar ya gana da wakilinmu a unguwar 'yan wasa ta gasar Olympic ta Beijing, inda ya bayyana yadda kasar Masar take share fagen aikin halartar gasar da yadda aka yi share fagen gasar.

Kungiyar wakilan wasannin motsa jiki ta Masar tana kunshe da 'yan wasa maza 69 tare da mata 31, kuma za su halarci kananan gasanni 18, ciki har da wasan kokawa da dambe da wasannin motsa jiki na zamani da ke kunshe da kananan wasanni biyar, wato wasan sukuwa da na ninkaya da na takobi da na harbi da gudu. Malam Shahin ya ce, yawan 'yan wasa ya fi yawa da kasar Masar ta aika wa gasannin Olympic, kuma yana gaban sauran kasashen Afirka da Larabawa. Amma lokacin da ya tabo magana kan yawan lambobin zinariya da kungiyar 'yan wasan Masar take nema, malam Shahin ya yi taka-tsan-tsan ya ce, "Kungiyar Masar tana fatan za ta iya samun wasu lambobi a gun wannan gasar Olympic, musamman za ta iya samun sabon cigaba a wasu gasannin da 'yan wasa na kasar Masar suke kwarewa sosai a cikin shekaru 4 da suka gabata. Alal misali, a gun wasannin motsa jiki da ke kunshe da kananan wasanni biyar na zamani, muna da Aya Medani, wato 'yar zakara ta duniya. Idan ta samu lambar zinariya a gun gasar Olympic ta Beijing, za ta zama zakara mace ta farko ta kasar Masar a gun gasannin Olympic."

Har sau da yawa ne Mr. Shahin ya jaddada cewa, domin kasancewar huldar sada zumunta ta gargajiya a tsakanin kasashen Masar da Sin, a bayyane ne gwamnatin kasar Masar ta ba da umurni cewa, dukkan 'yan wasa da suka samu izinin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing za su je Beijing domin shiga gasar gaba daya. Sabo da haka, kwamitin Olympic na kasar Masar ya yi dimbin aikin share fagen halartar wannan gasar Olympic ta Beijing. Ko da yake Karam Jabir wanda ya samu lambar zinariya a gun gasar daga nauyi ta wasannin Olympic na Athens na kasar Girka ya samu rauni a gun gasar neman izinin halartar gasar Olympic ta Beijing da aka yi a kasar Bulgaria, amma Mr. Shahin ya bayyana cewa, Mr. Karam Jabir zai halarci gasar Olympic ta Beijing.

"Bisa rahoton da likita ya bayar, Karam Jabir ya riga ya sami sauki. A gun gasar Olympic ta Beijing, zai fito a gun gasar daga nauyi."

Lokacin da ya tabo magana kan yadda kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya yi share fagen gasar Olympic ta Beijing, Mr. Shahin ya nuna yabo sosai. "Wannan ne karo na biyar da na halarci gasannin Olympic. Abin da nake son jaddadawa shi ne, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen neman samun nasarar shirya wata gasar Olympic. Sabo da haka, kasar Sin ta kara karfi sosai wajen kyautata ayyukan yau da kullum, kuma ta gina sabbin dakuna da filayen motsa jiki, kuma ta kan sanar da aikin da yake yi kan yadda yake share fagen gasar. Ban taba ganin irin wannan kokari ba a da. A waje daya kuma, a bayyane ne birnin Beijing ya samu sauye-sauye sosai. A matsayin daya daga cikin mutanen da suka gano irin wannan sauye-sauye, ina tsammani cewa, wannan gasar Olympic za ta zama wata gasar Olympic mafi kasaita."

A ganin Shahin, idan an kwatanta ta da sauran gasannin Olympic na da, abin da ya fi shan bamban a gun gasar Olympic ta Beijing shi ne jama'ar kasar Sin suna halartar ayyukan gasar Olympic cike da annashuwa. "Kwamitin shirya gasar Olympic ta Beijing ya samu nasara sosai wajen mayar da dimbin Sinawa da su halarci ayyukan da suke da nasaba da wasannin Olympic. Direbobi da dalibai da masu sayar da kayayyaki a kantuna da dai sauran mutane sun yi kokari sosai wajen ayyukan da suke da nasaba da gasar Olympic. Wannan ne nasara sosai da kwamitin shirya gasar Olympic ta Beijing ya samu, zai amfana wa aikin yada ruhun Olympic da mayar da jama'a da su halarci gasar Olympic."

Game da batutuwan ingancin iskar Beijing da na abinci da suke jawo hankulan 'yan wasa na kasashe daban daban, malam Shahin ya ce, "Wasu mutanen kungiyarmu suna nan Beijing. Ba wanda ya yi kuka kan ingancin iskar Beijing da ingancin abincin da ake samarwa a gun gasar ba. Akwai ire-iren abincin da ake samarwa a cikin unguwar 'yan wasanni ta gasar Olympic ta Beijing da ya kunshi kusan dukkan ire-iren abincin kasar Sin da na sauran kasashen duniya."