Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 19:52:38    
Tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun saurin karuwa ba tare da tangarda ba bayan wasannin Olympics

cri

Domin gasar wasannin Olympics ta Beijing tana ta kusantar halin koli, dimbin mutane sun fara nuna damuwa kan cewa, ko tattalin arzikin kasar Sin zai fuskanci matsalar karancin karfin samun bunkasuwa bayan gasar. Wang Yiming, mataimakin shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki daga manyan fannoni ta kwamitin cigaba da yin kwaskwarima na kasar Sin yana ganin cewa, bayan gasar wasannin Olympics, za a rage bukatun dimbin kudaden da aka zuba kan dakuna da filaye na motsa jiki da ayyukan yau da kullum da ke da nasaba da gasar kafin kaddamar da ita da kuma dimbin kudaden da masu yawon shakatawa na kasashen duniya suke kashewa a lokacin gasar nan da nan. Amma ainihin karfin raya tattalin arzikin kasar Sin a cikin shekaru 30 da suka gabata ba zai samu sauyi sosai ba. Yawan kudaden da aka zuba domin gasar wasannin Olympics ya yi kadan a cikin tattalin arzikin kasar Sin. Sabo da haka, gasar ba za ta zama wani al'amarin da ke kawo wa tattalin arzikin kasar Sin illa ba, kuma ba za ta canja halin samun saurin bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa da kasar Sin ke samu ba. Kuma Mr. Wang ya kara da cewa, "Alal misali, jimlar tattalin arzikin birnin Beijing ta kai kashi 3.6 bisa kashi dari a cikin dukkan jimlar tattalin arzikin kasar Sin a shekara ta 2007. Yawan kudaden da Beijing ya kebe wajen gina filaye da dakunan wasannin Olympics da kuma raya muhimman ayyukan yau da kullum ya kai kimanin Yuan biliyan 300, in an kasa su cikin shekaru hudu, wato matsakaiciyar jimlar ta kai Yuan biliyan 75 a ko wace shekara, wadda ta kai kashi 0.55 zuwa kashi 1.06 bisa dari a cikin dukkan kadarorin zamantakewar al'ummarmu, shi ya sa tasirin da ya bayar ya yi kadan sosai."

A waje daya kuma, Mr. Wang ya amince da cewa, yayin da gasar wasannin Olympics ke kawo wa kasar Sin damar samun bunkasuwa, ita ma ta kawo wa kasar kalubale wajen bunkasuwar tattalin arziki. Sabo da haka, ya kamata a kara mai da hankali kan rawar da gasar ta taka wajen bunkasuwar tattalin arziki, da kuma fuskantar abubuwa marasa kyau iri daban daban da watakila za su bullo. Kuma Wang Yiming ya ce, "Ya kamata mu ci gaba da yada amfanin filaye da dakunan wasannin Olympics da kuma muhimman ayyukan yau da kullum da abin ya shafa domin kyautata ingancin zaman rayuwar jama'a. Haka kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne ya kamata mu yada hasashen uku na wasannin Olympics na Beijing, wato 'wasannin Olympics na kiyaye muhalli, da na kimiyya da fasaha, da kuma na zamantakewar al'adu'domin sa kaimi ga sauye-sauyen hanyar raya tattalin arziki. Bugu da kari kuma, ya kamata mu yi amfani da rawar da gasar ta taka wajen sa kaimi ga sha'anin ba da hidima na zamani."

Game da makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, Wang Yiming yana ganin cewa, kasar Sin na da babban boyayyen karfi, kuma ya kara da cewa, "Yanzu muna cikin matsakaicin lokaci wajen samun karuwar masana'antu, kuma matsayinmu na bunkasuwar birane bai kai matsakaicin matsayin duniya ba, matsakaicin yawan kudin GDP da ko wane mutum ya samu ya kai kimanin dala 2500 a shekara ta 2007, wanda ke da nisa da matsayin kasashe masu ci gaba sosai. Shi ya sa muna da babban boyayyen karfi wajen raya masana'antu da muhimman ayyukan yau da kullum da kuma birane."(Kande Gao)