Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 19:55:22    
'Yan wasan gudun Marathon na na kasar Kenya suna son samun lambar zinariya ta Olympic

cri

A ran 11 ga wata, 'yan wasa 3 na gudun dogon zango wato Marathon na rukuni na farko na kasar Kenya sun tashi zuwa Beijing. Kafin su tashi, sun gana da wakilanmu, yauzu sai ku saurari labarin da wakilnmu Mr. Wei Tong da Mr. Xie Yi suka ruwaito.

Kasar Kenya da ke gabashin Afirka ta shahara a gudun dogon zango da matsakaicin zango a duniya, 'yan wasan gudun dogon zango da yawa sun taba samun lambar zinariya a cikin gasannin matsayin duniya. Amma har zuwan yanzu, kasar Kenya ba ta taba samu lambar zinariya ta gudun Marathon ba, saboda haka, 'yan wasan gudun Marathon na kasar Kenya suna son samun lambar zinariya ta gudun Marathon kwarai.

'Yan wasa 7 na kasar Kenya za su shiga gasar gudun Marathon ta wasannin Olymipcs na Beijing. Kuma yawancinsu sun taba samun lambobi a cikin gasannin cin kofi na matsayin duniya. 'Yar wasa Marths Komu wadda ta taba zama zakara a cikin gasar cin kofin duniya da aka yi a birnin Paris ta ce, ko da yake za ta fuskanci 'yan wasan gudun Marathon da ke da karfin takara sosai daga sauran kasashe, amma dole ne za ta yi iyakacin kokari domin cin nasara. Ta ce, "Na yi horo sosai, ko shakka babu ina son samu lambar zinariya, amma wannan ba abu ne mai sauki ba. 'Yan wasa na kasar Habasha suna da karfin takara sosai, kuma ina fuskantar kalubale daga zakara ta gudun Marathon ta gasar Olympic ta Athens. Amma, zan yi iyakacin kokari domin samu lambar zinariya."

Wata 'yar wasa daban wato Selina Kosgey da taba samun lambar azurfa a cikin gasar zango na Bahrain na gasannin gudun Marathon na duniya da aka yi a shekarar 2003. Selina Kosgey ta ce, yanzu tana cikin kyakkyawan hali, kuma ta shirya sosai domin neman samu lamba.

Ban da haka kuma, kungiyar 'yan wasan gudun Marathon ta kasar Kenya tana da wasu "tsofaffin 'yan wasa". Catherine Ndereba wadda shekarunta sun kai 40 da haihuwa ta taba zama zakara a gasar gudun Marathon da aka yi a Osaka a shekarar 2006, kuma ta taba samun lambar azurfa a cikin gasar gudun Marathon ta wasannin Olympics na Athens. Dan wasa Robert Cheruiyot ya taba zama zakara a cikin gasannin gudun Marathon da aka yi a Boston har sau hudu. ko da yake ba su zama 'yan wasa na kuruciya, amma game da wasannin Olympics na Beijing, suna amincewa da kansu sosai.

Mr. David Letting malamin koyar da wasan gudun Marathon na kasar Kenya ya fayyace cewa, kafin watanni da dama, 'yan gudun Marathon na kasar Kenya sun fara yin horo na musamman, ya zuwa yanzu, ba su daina yin horo ba. Ya nuna cewa, "Ba kamar sauran wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ba, gudun Marathon shi ne gasar gudu mafi tsawo, yana bukatar hakuri da karfi masu yawa tare da saurin gudu. Za mu cigaba da yin horo bayan mu sauka kasar Sin domin tabbatar da samun kyakkyawan sakamako."

Mr. David ya ce, ya amince da 'yan wasa na kasar Kenya sosai. Ya ce, "Mun riga mun shirya sosai, muna jiran 'yan wasa na kasar Kenya su taka kyakkyawan ayyuka cikin gasanni. Na yi fatan alheri gare su, ina son za su samu lambar zinariya ta farko ta gasar gudun Marathon cikin wasannin Olympics."

A ran 17 ga wata, za a yi gasa ta karshe ta gudun Marathon na mata ta wasannin Olympics na Beijing, kuma za a yi gasa ta karshe ta gudun Marathon ta maza a ran 24 ga wata yayin da za a yi bikin rufewa. Muna fatan 'yan wasan kasar Kenya za su sami kyakkyawan sakamako.